CRI Hausa" />

Kasar Sin Ba Ta Samu Tallafin Da Kasar Amurka Ta Yi Alkawarin Samar Mata Ba

Geng Shuang, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce ko da yake wasu manyan jami’an Amurka sun bayyana a wurare daban daban cewa, kasarsu za ta samar da daukin da darajarsa ta kai dalar Amurka miliyan 100 ga kasar Sin da sauran kasashe, don taimakawa kokarinsu na dakile yaduwar cutar COVID-19, amma har zuwa yanzu, a cewar jami’in na Sin, kasar Sin ba ta samu wani tallafi daga gwamnatin Amurka ko kobo daya ba.

Da yake bayyana haka jiya a nan birnin Beijing, Geng Shuang, ya ce la’akari da cewa an riga an samu gagarumin ci gaba a kasar Sin, a fannin hana yaduwar cutar COVID-19, yayin da sauran kasashe daban daban ke fama da barkewar annobar, kasar Sin ta riga ta godewa Amurka, tare da bukatar ta gaggauta mika tallafin da ta yi alkawarin ba ta, ga sauran kasashen da suke da bukata matuka.
Ban da haka kuma, game da jita-jitar da ake yadawa cewa, kayayyaki kirar kasar Sin na dauke da kwayoyin cuta, da kiran wai daina sayen kayayyakin kasar Sin da wasu mutane suka yi. Kakakin na ma’aikatar wajen kasar Sin ya karyata zancen, tare da yin Allah wadai da wasu mutanen da ke neman ta da hankalin jama’ar kasashe daban daban.
Ya ce, a wannan yakin da daukacin bil Adama suke yi da kwayoyin cutar COVID-19, ya kamata a mutunta kimiyya da fasaha, da sauran mutane. Sa’an nan abin da ya fi muhimmanci shi ne tsare mutumcin kai. (Mai Fassarawa: Bello Wang)

Exit mobile version