CRI Hausa" />

Kasar Sin Ba Ta So Maye Gurbin Amurka

Kwanan nan, akwai wasu ’yan siyasar kasar Amurka dake cewa, “Tattalin arzikin kasar Sin yana kamo na Amurka cikin sauri, don haka kasar Sin za ta fi Amurka karfi”, kana sun ce, “kada ma kasar Sin ta yi tunanin zama kasar da ta fi kowa karfi a duniya”. A hakika, kasar Sin ba ta taba tunanin maye gurbin Amurka a matsayin burinta na samun ci gaba ba. Irin wannan ra’ayi maras kan gado da wasu ’yan siyasar Amurka ke da shi na mayar da kasar Sin a matsayin abokiyar gaba, ya nuna cewa, suna damuwa sosai kan manyan tsare-tsaren kasar su.
Tun bayan kawo karshen yakin cacar baki, kasar Amurka ta tabbatar da matsayinta na babbar kasa mafi karfi daya tilo a duniya. Ya zuwa yanzu ita ce take kan gaba a fannonin tattalin arziki, kudi, kimiyya da fasaha, aikin soja da dai sauransu. Alkaluman kididdiga da cibiyar nazarin zaman lafiyar kasa da kasa ta Stockholm ta fitar a shekarar 2018 sun nuna cewa, yawan kudin da kasar Amurka ta kashe a fannin aikin soja ya wuce dala biliyan 640, hakan ya sa kasar ta zama na farko a duniya a wannan fanni, kuma yawan kudin da ta kashe a wannan fannin ya yi daidai da jimilar kudin da kasashe guda takwas dake bayanta suka kashe a wannan bangare.

Duk da haka, akwai wasu Amurkawa wadanda ke ganin cewa ba su da cikakken tsaro.
Tun bayan da kasar Sin ta shafe tsawon shekaru arba’in tana aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, tattalin arziki gami da kimiyya da fasahar kasar na bunkasa cikin sauri. Duk da cewa akwai babban gibi tsakanin Sin da Amurka, amma gibin na dada raguwa.
Dalilin da ya sa wasu ’yan siyasar Amurka suke adawa da kasar Sin shi ne, domin irin babakaren da suka dade suna yi na fuskantar babbar adawa yayin da duniya ke dunkulewa waje guda. Hakan ya sa suke damuwa sosai kan cewa kasar Sin za ta zarce Amurka. Har wa yau, nuna kiyayya ga kasar Sin zai taimaka wajen warware matsalolin da suke fuskanta a kasarsu, ta yadda wasu mutane za su ci gajiya. Game da hakan, tsohon shugaban kasar Amurka Jimmy Carter ya nuna cewa, bai damu kan cewa kasar Sin za ta zarce kasar Amurka har ma ta zama kasa mafi karfi a duniya ba, ainihin matsalar Amurka ita ce tana son tada yaki sosai.

Kwatan kwacin kasar Amurka, al’ummar Sinawa na da al’adar cewa, kasa kome girmanta, za ta ruguje idan kullum abin ke gabanta shi ne tada yaki. Duk da cewa kasar Sin yanzu haka ita ce kasa ta biyu a duniya a fannin karfin tattalin arziki a duniya, amma har yanzu kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya. A bara, yawan GDPn kowane dan kasar Sin ya kai kusan dala dubu 10, adadin da bai kai kaso daya daga cikin shida na Amurka ba. baya ga haka, akwai mutane sama da miliyan 16 dake fama da talauci a kasar.
Aikin da kasar Sin taka sanya a gaba shi ne raya tattalin arzikinta, ta yadda al’ummarta za su kara jin dadin rayuwa. Kasar Sin na mai da hankali ne a kan abubuwan da ta sanya a gabanta, kuma ba ta da niyyar maye gurbin Amurka, balle ma a ce ta yi mummunar takara da wasu kasashe. Kasar Sin ba ta da ra’ayin nuna fin karfi, kuma tana bin manufar raya harkokinta cikin lumana, matakin da za ta kara samar da damar bunkasuwa ga kasashe daban daban. (Masu fassarawa: Bilkisu, Murtala, Lubabatu, ma’aikatan sashen Hausa na CRI)

Exit mobile version