Kasar Sin ta bayyana matukar adawa da zarge-zargen kungiyar G7 kan tekun kudancin kasar da manufofinta na tattalin arziki, kuma ta bayyana korafinta ga kasar Canada.
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Canada ne ya bayyana haka a yau Asabar.
A cewar ofishin jakadancin, sanarwar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 da sanarwar ministocin game da tsaron teku, sun yi shisshigi cikin harkokin gidan Sin, kana sun bata mata suna. (Fa’iza Mustapha)