Kasar Sin Na Gaggauta Gwajin Kudin Yuan Na Intanet Domin Wasannin Olympics Na Lokacin Hunturu

Daga CRI Hausa,

An shiga mataki na karshe na aikin samar da tashoshin biyan kudin yuan na intanet yayin wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing na 2022, a wani bangare na inganta sabon tsarin biyan kudi na kasar.

Babban Bankin kasar Sin, ya ce an kammala ginin dukkan wuraren biyan kudin yuan ta intanet a ofisoshin kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing na 2022, da wasannin Olympics na nakasassu na lokacin hunturu.

Akwai tashoshin biyan kudi a dukkan wuraren wasa na Zhangjiakou dake lardin Hebei. Sauran wuraren dake yankin Zhangjiakou kuma, sun sanya hannu kan kwangila ko suna shirye-shiryen samar da wuraren.

Masu sayayya na iya amfani da kudin yuan na intanet ko ta hanyar asusun dake manhajojin wayar salula ko kuma katunan bankin da sauran abubuwa kamar agoguna masu kwakwalwa da safar zamiyar kankara da baji, domin biyan bukatunsu.

Za kuma su iya samun asusun ajiyar kudin yuan na intanet a rassan bankin China da nau’rori bayar da hidima irin na ATM da wasu otel otel. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

Exit mobile version