Kasar Sin Ta Fitar Da Jirgin Kasa Mafi Sauri A Duniya

Daga CRI Hausa

A yau Talata, sabon jirgin kasa mai matukar sauri da kasar Sin ta samar ya bayyana, wanda ke nufin ya fita daga matakin kira.

Jirgin mai amfani da karfin maganadisu, na tafiyar kilomita 600 cikin kowacce sa’a, lamarin da ya sanya shi zama abun hawa mai tafiya a kan kasa mafi sauri a duniya.

Sabon jirgin ya bayyana ne karon farko a yau, a birnin Qindao na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin.

A cewar hukumar samar da jiragen kasa ta kasar Sin, kasar ce ta kirkiro jirgin da kanta, wanda ke zaman sabon gagarumin ci gaban kimiyya da fasaha da ta samu a fannin sufurin jiragen kasa. (Fa’iza Mustapha)

Exit mobile version