Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira da a karfafa harkokin cinikayya da kasashen waje, bisa ruhin kirkire-kirkire da jan ragamar bangaren, tare da gaggauta samar da sabon karfin bude kofa.
Li Qiang ya bayyana haka ne lokacin da yake rangadi a lardin Fujian na kudu maso gabashin kasar Sin, daga ranar Talata zuwa jiya Alhamis.
Firaministan ya yi kira da kada a yi kasa a gwiwa wajen fadada bude kofa da raya kasuwanni daban-daban da kuma kirkiro sabbin dabaru da hanyoyin kasuwanci.
Da yake bayyana kamfanoni masu zaman kansu a matsayin jigon kasar Sin na cinikayya da kasashen waje, Li Qiang ya ce ya kamata gwamnatoci a dukkan matakai, su yi kokarin samar da ingantattun manufofin tallafi da kyakkywan muhallin raya harkokin kasuwanci masu zaman kansu. (Fa’iza Mustapha)