Kasar Sin ta kara azamar kirkiro da fasahar sadarwa mai karfin 6G a cikin ’yan shekarun nan, inda ta samu ci gaba a bangaren binciken fasalin tsarin fasahar ta 6G da kuma zayyanar hanyar sadarwarta, kamar yadda ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta zamani ta kasar ta bayyana a jiya Alhamis.
A yayin gudanar da taron bunkasa fasahar 6G na shekarar 2025, mataimakin ministan masana’antu da fasahar sadarwa ta zamani na kasar Sin Zhang Yunming ya bayyana cewa, yanzu haka kasar tana da muhimman fasahohi na kirkiro da fasahar sadarwar 6G sama da 300.
Zhang ya kara da cewa, kasar ta hada kan kamfanoni sama da 100 na cikin gida da na waje a fannin tsarin masana’antu, kuma ta gayyaci kamfanonin duniya su zo su shiga cikin gwajin da ake yi na fasahar 6G.
Zhang ya yi nuni da cewa, a wannan shekarar an fara gudanar da cikakken bincike kan tabbatar da ingancin fasahar 6G, inda ya kara da cewa yanzu haka aikin kirkiro da fasahar 6G yana kan wani muhimmin mataki wanda ke bukatar hikima da kuma cimma matsaya guda. (Abdulrazaq Yahuza Jere)












