Kasar Sin Ta Kasance Mai Hangen Nesa Da Samarwa Kanta Mafita A Duk Lokacin Da Ake Mata Zagon Kasa
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Ta Kasance Mai Hangen Nesa Da Samarwa Kanta Mafita A Duk Lokacin Da Ake Mata Zagon Kasa

byCMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar da sabbin matakan daukaka tattalin arzikin kasar da ma ingancin kayayyakin da aka kera a kasar.

A yanzu haka, kasar Sin ce babbar mai bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin duniya duk da kalubale da rashin tabbas da ake fuskanta a duniya. Don haka, kara karfafa tattalin arzikinta fiye da yadda yake a yanzu, zai bayar da gagarumar gudunmawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya da ma kasashe masu tasowa.

  • An Samar Da Damar Dawo Da Zirga-zirga A Dukkan Fannoni A Tsakanin Hong Kong Da Babban Yankin Kasar Sin

A cewar sanarwar da majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar jiya, zuwa shekarar 2025, za a bunkasa ingancin kayayyaki kirar kasar Sin. A yanzu haka, kayayyakin kasar Sin sun karade ko ina a fadin duniya, kusan babu gidan da za a shiga ba tare da ganin wani abu da kasar Sin ta kera ba, wannan yana nuna irin nasarar da Sin ta samu wajen kera kayayyaki masu inganci da kuma rahusa. A ganina, hauhawar farashin kayayyaki da aka samu a baya-bayan nan a kasashe masu tasowa har ma da manyan kasashe, na da nasaba da matakan yaki da annobar COVID-19. Amma bisa la’akari da sabbin matakan da Sin ta dauka, da kuma aka riga aka fara aiwatarwa a bana, ba makawa, za a samu sauki a fadin duniya, kuma kasashe masu tasowa za su samu damar amfana daga kayayyaki masu inganci da masana’antun kasar Sin za su samar.

Haka kuma sanarwar ta ce, kasar za ta inganta takarar masana’antu. A lokacin da ake kokarin dakile masana’antun kasar Sin ta kowacce fuska, wannan mataki zai kara karfafa musu gwiwa da kara samar musu da dimbin damarmaki a duniya, ta yadda babu wanda zai iya dakile su. Karfin takarar da za su yi da takwarorinsu na duniya, zai kara musu tagomashi da kasuwa da kuma samun karbuwa.

Hakika kasar Sin ta kasance mai hangen nesa a ko da yaushe, inda take samarwa kanta mafita a duk lokacin da ake kokarin dakile ta. Haka kuma ta kan mayar da hankali ne ainun wajen inganta kanta a cikin gida ba tare da kokarin dakile wani bangare ko yin zagon kasa ba. Shi ya sa har kullum take kara samun tagomashi da farin jini a duniya, abun da ya kamata sauran kasashe su nazarta domin su yi koyi da shi don tsayawa da kafarsu da samun ci gaba ba tare da dogaro da wani bangare ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Next Post
Sauyin Kudi: Bankin Zenith Ya Rufe Wasu Rassansa A Nijeriya Sakamakon Kai Masa Hari

Sauyin Kudi: Bankin Zenith Ya Rufe Wasu Rassansa A Nijeriya Sakamakon Kai Masa Hari

LABARAI MASU NASABA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version