Kasar Sin Ta Sake Bayyana Matsayinta Kan Rahoton Ofishin OHCHR Dangane Da Jihar Xinjiang
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Ta Sake Bayyana Matsayinta Kan Rahoton Ofishin OHCHR Dangane Da Jihar Xinjiang

byCMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya sake bayyana matsayin kasarsa, kan rahoton da ofishin babban kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya mai lura da hakkokin bil’adama, ko kuma OHCHR a takaice ya fitar, wanda ya shafi jihar Xinjiang ta kasar Sin, tare da kira ga kasashe membobin MDD da su dora laifi kan OHCHR.

Zhao Lijian ya ce, rahoton cike yake da karairayi, wanda kasar Amurka tare da sauran wasu kasashen yammacin duniya suka kirkiro don cimma muradunsu na siyasa, kana, ya sake shaida cewa, ofishin OHCHR ya riga ya zama mai hada baki da Amurka, da sauran wasu kasashen yamma wajen lalata kasashe masu tasowa.

  • Sin: Ya Kamata Amurka Ta Yi Watsi Da Molon Ka Ta Rungumi Abubuwa Masu Amfani Don Samar Da Daidaito Da ‘Yancin Bil Adama

Zhao ya kara da cewa, kwanan nan ne kasashe sama da 60, suka gabatar da sako zuwa ga ofishin OHCHR, inda suka jaddada cewa, batun jihar Xinjiang, batun cikin gidan kasar Sin ne zalla, don haka sun nuna matukar damuwa kan irin wannan rahoton da ofishin ya rubuta ba tare da samun izini daga kasar Sin ba.

Haka kuma kungiyoyin da ba na gwamnati ba kusan dubu 1 na gida da na waje, sun rubuta wasika ga OHCHR, inda suka nuna adawarsu kan abun da ofishin ya yi, wato gabatar da wani rahoto game da Xinjiang wanda ya jirkita gaskiya.

Zhao ya kuma nuna cewa, a matsayinsa na wani sashi na sakatariyar MDD, ya zama dole OHCHR ya girmama ka’idojin tsarin mulkin majalisar, kana, bai kamata ya yi shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasashe membobinta ba.

Amma rahoton da OHCHR ya fitar game da Xinjiang, wanda ke karkashin makircin Amurka da sauran wasu kasashen yammacin duniya, ya saba wa hakan. (Murtala Zhang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
…Dalla-dallar Yadda Aka Kashe Kudin Tallafin Mai

…Dalla-dallar Yadda Aka Kashe Kudin Tallafin Mai

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version