Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Kasar Sin Ta Sake Tura Kayayyakin Kandagarkin Cuta Zuwa Afrika Ta Tsakiya Da Guinea-Bissau

Published

on

A ranar 11 ga wata bisa agogon jamhuriyar Afrika ta tsakiya, an gudanar da bikin mika kayayyakin kandagarkin cutar COVID-19, da kasar Sin ta baiwa kasar a matsayin tallafi jeri na 2, a filin saukar jiragen sama dake Bangui, fadar mulkin kasar. Inda shugaban kasar Afirka ta Tsakiya Faustin Touadera, da jakadan kasar Sin a kasar Chen Dong, gami da sauran manyan kusoshin sassa daban daban, suka halarci bikin.

A wajen bikin, shugaba Touadera ya shaidawa jakada Chen na kasar Sin cewa, gwamnatin kasar Sin da jama’arta, sun kai dauki ga jama’ar kasar Afirka ta Tsakiya, jim kadan bayan sun tsunduma cikin mawuyacin hali na fama da annoba, saboda haka yana matukar godiya ga kasar Sin.
A nasa bangaren, ministan lafiya na kasar Afirka ta Tsakiya, mista Pierre Somse, ya ce, kasarsa ba za ta samu ainihin alkaluma game da yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 ba, balle ma jinyarsu da kubutar da su, in ba dan na’urorin gwajin cuta da kasar Sin ta ba ta ba. Saboda haka, a cewarsa, samun goyon baya daga kasar Sin, shi ne tushen aikin yakar cutar COVID-19 a kasar Afirka ta Tsakiya.
A nasu bangare, kamfanonin kasar Sin 4 dake kasar Guinea-Bissau sun bada gudunmawar na’urorin taimakon numfashi 2, ga hukumomin lafiya na kasar, domin taimaka musu jinyar masu cutar COVID-19.
Yayin bikin mika gudunmawar, Jakadan kasar Sin a Guinea-Bissa, Jin Hongjun, ya nanata kudurin gwamnatin kasar Sin na ci gaba da tallafawa al’ummar Guinea-Bissau a yakin da suke da COVID-19.
Jakadan ya kara da cewa, a mako mai zuwa, wani karin gudunmawar kayayyakin lafiya daga gwamnatin kasar Sin za ta isa Guinea-Bissau. Yana mai cewa, gudunmawar dake tafe, za ta taimaka wajen inganta yanayin aiki ga jami’an lafiya.
Bugu da kari, ya ce goyon bayan juna na da muhimmanci gaya wajen fatattakar cutar, wadda ta zama abokiyar gabar bil adama. Yana mai cewa, gudunmawar da kamfanonin kasar Sin suka bayar, alamu ne na goyon baya. (Bello Wang / Fa’iza Mustapha)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: