Yau Asabar, kwamitin kula da raya kasa da aiwatar da gyare-gyare ta kasar Sin (NDRC), ta ce ta ware yuan miliyan 100, kwatankwacin dala miliyan 13.95, kari kan yuan miliyan 100 da ta ware a ranar Larabar da ta gabata, domin taimaka wa ayyukan agaji a kudu maso yammacin Sin.
Mummunar ambaliyar ruwa ta sake dawowa a gundumar Rongjiang ta lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin, lamarin da ya sanya hukumomin wurin sake ayyana matakin koli na tunkarar ambaliya, daga karfe 12:30 na rana a yau.
Hukumomi a yankin na kwashe mazauna daga wuraren da lamarin ya shafa. Zuwa karfe 6 na yamma, gundumar ta tsara aikin gaggawa na kwashewa tare da tsugunar da iyalai 11,992 da daidaikun mutane 41,574.
Tun daga ranar 24 ga wata, gundumar Rongjiang ke fama da mummunar ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama. (Fa’iza Mustapha)