Masana kimiya na kasar Sin, sun yi nasarar kafa wani tsarin sadarwa da ya kunshi wayoyin sadarwa 700 da taurarin dan-Adam biyu da aka girke a kasa, wadanda za su iya hade sama da masu cin gajiyar tsarin 150 bisa nisan da ya kai kilomita 4,600.
Pan Jianwei na jami’ar kimiya da fasahar kere-kere ta kasar Sin, shi ne ya jagoranci shirin binciken, da wani rukunin masana suka gudanar a shekarun da suka gabata. An kuma wallafa takardar sakamakon binciken a mujallar kimiya ta Nature da ake wallafawa ta yanar gizo.
Tsarin sadarwar ya kunshi, hanyoyin sadarwa na zamani da ya hade birane (QMAN), ciki har da Beijing, da Jinian, da Hefei da Shanghai, babban layin da ya kai nisan sama da kilomita 2,000. Akwai kuma taurarin dan-Adam guda biyu da suka hade tashar Xinglong dake Beijing da tashar dake Nanshan dake Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa na kasar Sin, wadanda ke da tazarar kilomita 2,600 a tsakaninsu. An kuma hade Xinglong da hanyar sadarwar zamani ta Beijing ta wayar sadarwa.(Ibrahim)
Gyara Kayanka Baya Zama Sauke Mu Raba
Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitinta na sulhu, sun yi kakkausar...