Kasar Sin Ta Samu Cikakkiyar Nasarar Yaki Da Talauci

Talauci

лªÉçÕÕƬ£¬±±¾©£¬2021Äê2ÔÂ25ÈÕ È«¹úÍÑƶ¹¥¼á×ܽá±íÕôó»áÔÚ¾©Â¡ÖؾÙÐÐ 2ÔÂ25ÈÕ£¬È«¹úÍÑƶ¹¥¼á×ܽá±íÕôó»áÔÚ±±¾©ÈËÃñ´ó»áÌáÖؾÙÐС£ лªÉç¼ÇÕß Ò󲩹ŠÉã

Daga Jamila Zhou,

A ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata, kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwa ta kasar sun kira babban taron yabawa wadanda suka ba da babbar gudunmawa wajen kawar da talauci a nan birnin Beijing, inda shugaban kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin ta samu cikakkiyar nasara wajen kawar da talauci bayan kokarin da daukacin al’ummun kasar suka yi a cikin shekaru takwas da suka gabata, bisa ma’auni na yanzu, manoman kauyuka dake fadin kasar kusan miliyan 100 wadanda suka taba fama da talauci sun fita daga kangin talauci daga duk fannoni, a sa’i daya kuma, ya jaddada cewa, akwai bukatar a ci gaba da yin kokari domin farfado da tattalin arzikin kauyuka, tare kuma da rage gibi dake tsakanin kauyuka da birane.

Tun farkon kaddamar da babban taron, shugaba Xi ya sanar da cewa, “Yau, mun kira wannan gagarumin taro domin sanar da cewa, mun samu cikakkiyar nasarar yaki da talauci, bayan kokarin da daukacin al’ummun kasar suka yi, bisa ma’auni na yanzu, gaba daya manoma dake kauyuka da yawansu ya kai miliyan 98 da dubu 990 sun fita daga kangin talauci, kuma an fitar da daukacin gundumomi 832 da kauyuka dubu 128 daga wadanda suke fama da talauci, kasar Sin ta cimma burin kawar da talauci a fadin kasar, ana iya cewa, ta yi wani abin al’ajabi a tarihin bil Adama.”

A cikin shekaru takwas da suka gabata, adadin mutanen da suka fita daga kangin talauci a kasar Sin a ko wace shekara ya kai miliyan 10, ba ma kawai kudin shigarsu ya karu ba, har ma rayuwarsu ita ma ta kyautata, shugaba Xi ya bayyana cewa, “Kudin shigarsu ya karu a bayyane, kuma suna samun isasshen abinci da sutura, kana an tabbatar da hakkinsu na samarwa ‘yayansu ilmi kyauta da inshurar jinya da gidajen kwana mai inganci.”

Fasahohin kawar da talauci na kasar Sin, za su taka rawa a aikin rage talauci a duniya, shugaba Xi yana mai cewa, “Muna nuna kwazo da himma domin gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya wajen rage talauci, kuma muna samar da tallafi gwargwadon karfinmu ga kasashe masu tasowa, kasar Sin tana ba da gudummawarta ga yunkurin gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya. Nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakai domin tabbatar da sakamakon yaki da talauci da ta samu, tare kuma da ingiza farfadowar tattalin arzikin kauyukan kasar daga dukkan fannoni.”

To, kamar yadda aka sani, batun rage talauci babbar matsala ce da ta dade tana addabar daukacin kasashen duniya, musamman ma a shekarar 2020 da ta gabata, inda al’ummun kasashen duniya suka fama da yaduwar annobar cutar COVID-19 da kuma matsalar sauyin yanayi, an lura cewa, a cikin shekarar da ta gabata, adadin mutanen da suka yi fama da kangin talauci mai tsanani a fadin duniya ya karu a karo na farko tun bayan shekaru sama da ashirin da suka gabata, sakamakon matsalolin da COVID-19 da sauyin yanayi suka haifar.

A don haka an fi mai da hankali kan wane misalin da kasar Sin ta kawo wa aikin rage talauci a duniya.

Adadin al’ummun kasar Sin ya kai kaso 20 bisa dari na daukacin al’ummun kasashen duniya, a don haka ana iya cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu wajen yaki da talauci ba sakamako ne na kasar Sin kawai ba, sakamako ne na duniya baki daya.

A matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin ta yi nasarar kawar da talauci daga dukkan fannoni, lamarin da ya kara karfafa wa sauran kasashe gwiwa a fannin kawar da talauci. Shugaban hukumar yankin Asiya da tekun Pasifik ta asusun raya aikin gona na duniya Nigel Brett ya bayyana cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu ya shaida cewa, kawar da talauci ba mafarki ba ne, ana iya cimma burin idan aka yi kokari.

Abu mafi muhimmanci shi ne, misalin da kasar Sin ta bai wa sauran kasashen duniya ya samar da fasahohi masu ma’ana ga duk duniya.

A sa’i daya kuma, matakan da kasar Sin ta dauka sun taimakawa ajandar samun dauwamammen ci gaba ta MDD nan da shekarar 2030, a don haka ya dace sauran kasashen duniya su yi nazari kan fasahohin kasar Sin a wannan bangare, ta yadda za mu gina duniyarmu, da babu talauci tare.

Hakika al’ummun Sinawa sun yi abin al’ajabi a yaki da talauci ne a tarihin bil Adama.

Duba da cewa, babu wata kasa a duniya wadda ke iya cimma burin fitar da al’ummu sama da miliyan 100 daga kangin talauci a cikin gajeren lokaci kamar haka, musamman ma a cikin shekaru takwas da suka gabata, amma kasar Sin ta fitar da mutane miliyan 10 daga kangin talauci a cikin kasar a ko wace shekara, saurin da ya burge al’ummun kasashen duniya matuka.

A cikin rahoton da ya gabatar yayin babban taron yabawa wadanda suka ba da babbar gudunmawa wajen kawar da talauci da aka kira, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya waiwayi tarihin yaki da talauci na kasar, inda ya tattara fasahohin da kasar Sin ta samu daga fannoni bakwai, wadanda suka kunshi nacewa kan jagorancin JKS, da nacewa kan tunanin mayar da moriyar al’ummun kasa da farko, da nacewa kan tsarin gurguzu da sauransu.

Hakika sakamakon da kasar Sin ta samu wajen yaki da talauci, ya nuna sakamakon da ta samu wajen kare hakkin bil Adama, matakin da zai ciyar da aikin yaki da talauci a duniya gaba yadda ya kamata. Wakilin asusun raya aikin gona na duniya na MDD dake kasar Sin Matteo Marchisio shi ma ya bayyana cewa, kasar Sin ta shaida cewa, yaki da talauci ba mafarki ba ne, ana iya cimma burin a zamanin da muke ciki, kuma wannan muhimmiyar rawa ce da kasar Sin ta taka a aikin rage talauci a duniya.

Kana a ranar 28 ga watan Fabrairun da ya gabata, manyan masanan kasar Sin sun fitar da wani rahoto mai taken “Ilmin rage talauci na kasar Sin”, inda suka yi cikakken bayani kan manyan nasarorin da kasar Sin ta samu wajen yaki da talauci, da dabarun yaki da talauci masu tsarin musamman na kasar Sin, da ma’anar sakamakon da kasar Sin ta samu ga sauran kasashen duniya, ta hanyar yin amfani da ilmin siyasa da tattalin arziki.

A cikin shekarar 2020, duk da cewa, daukacin bil Adama sun sha wahalhalu da dama, sakamakon bazuwar annobar COVID-19 da kuma matsalar sauyin yanayi, amma kasar Sin ta cimma burinta na kawar da talauci daga dukkan fannoni a fadin kasar, haka kuma ta cimma burin rage talauci da aka tsara a ajandar samun dauwamammen ci gaba nan ta MDD nan da shekarar 2030 kafin shekaru goma, babban abin al’ajabi ne bisa saurin kammala aikin da adadin mutanen da aka fitar daga kangin talauci.

A halin da ake ciki yanzu, kasashen duniya suna kokari domin neman samun dabarun rage talauci da suka dace da hakikanin yanayin da suke ciki, masanan kasa da kasa da suke nazarin aikin rage talauci, suna ganin cewa, kasashen duniya suna iya koyon fasahohin rage talauci na kasar Sin, inda suka bayyana cewa, abu mafi muhimmanci yayin da kasar Sin take kokarin yaki da talauci shi ne, nacewa kan jagorancin JKS.

A cikin rahoton, manyan masanan kasar Sin sun yi nuni da cewa, fasahohin rage talaucin kasar Sin sun kunshi fannoni guda biyar, wato nacewa kan jagorancin JKS mai karfi, da tsara cikakken tsarin yaki da talauci, da tsara manufofin raya kasa, da gudanar da harkokin da abin ya shafa ta fasahohin zamani, da kuma aiwatar da shirin bisa matakai daban daban, inda aka mayar da jagorancin JKS a matsayin koli, saboda ana ganin cewa, muddin jam’iyya mai rike mulkin kasa tana da karfi, kuma ta fitar da manufofin da suka dace da babbar moriyar al’ummar kasa, hakika za a cimma burin yaki da talauci a kasar.

Hakazalika, har kullum kasar Sin tana nacewa kan manufar more sakamakon ci gaba tare, wato ana samar da damar more sakamakon ci gaba ga masu fama da talauci, hakika tun farkon kafuwar JKS, jam’iyyar ta kuduri aniyar cewa, za ta yi kome domin jama’a, kuma za ta yi kome bisa dogarar jama’a, wannan manufa ce da take aiwatarwa a cikin shekaru dari daya da suka gabata. A cikin rahoton babban taron wakilan JKS karo na 19, an yi nuni da cewa, JKS ta yi alkawari cewa, za ta gina tsarin rayuwa mai matsakaicin wadata ga al’ummun Sinawa, kuma ba za a bar ko wanen Basine a baya ba, kuma kasar Sin tana son more fasahohin yaki da talaucin da ta samu tare da sauran kasashen duniya, ta yadda za a fuskanci sabon kalubalen daidaita matsalar talauci a fadin duniya tare da sauran kasashe. (Marubuciya: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version