Kasar Sin Ta Yi Cikakkiyar Nasarar Harba Kumbon Shenzhou-13

Daga CRI Hausa,
A sanarwar ofishin kula da ayyukan sararin samaniyar kasar Sin, da misalin karfe 12 da mintoci 23 na tsadar daren Asabar wato ranar 16 ga wata bisa agogon Beijing, an harba rokar LongMarch-2F da ke dauke da kumbon Shenzhou-13 bisa lokacin da aka tsara a cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan.

Bayan kimanin dakika 582 kuma, kumbon Shenzhou-13 din ya yi nasarar rabuwa da rokar, sannan ya shiga inda aka kayyade. An yi nasarar tura ‘yan sama jannati uku, da suka hada da Zhai Zhigang, Wang Yaping, da Ye Guangfu zuwa sararin samaniya, yanzu dai suna cikin koshin lafiya.

Wannan aiki shi ne karo na 21 tun bayan tabbatar da gudanar da ayyukan sararin samaniya masu dauke da ‘yan saman jannati na kasar Sin, kana aiki na biyu mai dauke da ‘yan sama jannati ne a matakin tashar sararin samaniya na ayyukan.

Bayan da kumbon Shenzhou-13 ya shiga hanyar da aka tsara a sararin samaniya, ya kuma yi nasarar hadewa da babban akwatin Tianhe. Da karfe 9:58 na safiyar ranar 16 ga watan Oktoba na shekarar 2021 bisa agogon Beijing, ‘yan sama jannatin uku sun shiga cikin babban akwatin Tianhe daya bayan daya, hakan ya nuna yadda tashar sararin samaniya ta kasar Sin ta yi maraba da rukunin ma’aikata na biyu da ‘yar sama jannati ta farko.

A nan gaba, ‘yan sama jannatin za su gudanar da ayyukansu kamar yadda aka tsara. (Mai fassara: Bilkisu)

Exit mobile version