Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Kasar Sin Ta Yi Gargadi Game Da Yiwuwar Ambaliya A Lokacin Damina

Published

on

Mataimakin ministan albarkatun ruwa na kasar Sin Ye Jianchun, ya yi gargadi game da tsanantar yanayi a lokacin damina, inda ya bukaci dukkan sassan da abin ya shafa, da su shiryawa yiwuwar manyan ambaliyar ruwa.

Da yake karin haske yayin taron manema labarai da aka shirya a Alhamis, ya ce, a yayin da kasar Sin ta shiga lokaci na manyan ambaliyar ruwa, akwai koguna 148 da suka zarce mizanin gargadi na yin ambaliya.
A cewar ma’aikatar, a wannan shekarar, an yi ruwan sama masu karfin gaske sau 18. Kana daga ranar 2 ga watan Yuni zuwa wannan lokaci, akwai larduna 12 da suka samu ambaliya, abin da ya kai sama da milimita 400 na ruwa a yankin da ya kai sama da muraba’in kilomita 24,000.
Ye ya ce ma’aikatarsa ta bukaci kananan hukumomi, da su shirya matakan kare rayukan jama’a, koda wadanda ake da su, ba za su iya jure ambaliyar da za a iya samu ba.
Haka kuma, ma’aikatar tana aiki da sauran hukumomi, don inganta tsarin gargadi, don tabbatar da cewa, mutanen dake zaune a wurare mafiya hadari, sun samu gargadi a kan lokaci.
Bisa wani labarin da aka bayar a Alhamis, an ce, sama da mutane 20 sun mutu ko kuma sun bace bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sheka wanda ya yi sanadiyyar ambaliyar ruwa da zaftarewar laka a kudancin kasar Sin, bisa ga rahoton da jami’an yankin suka fitar.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar Sin ta ce, ya zuwa karfe 2 na yammacin ranar Talata, an samu mamakon ruwan sama wanda ya haifar da ambaliyar ruwa kuma ya shafi mutane kusan miliyan 2.63 daga larduna 11.
A cewar ma’aikatar, ruwan saman da aka sheka ya sa an sauya matsugunai ga mutane kimanin 228,000, sannan gidaje sama da 1,300 sun lalace, lamarin da ya haddasa hasarar tattalin arziki na sama da yuan biliyan 4 kwatankwacin dala miliyan 566. (Masu Fassarawa: Ibrahim Yaya, Ahmad Fagam)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: