CRI Hausa" />

Kasar Sin Ta Yi Kira Da Hadin Kai Wajen Samar Da Makoma Mai Kyau Ga Bil Adama

Bil Adama

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi kira ga dukkan kasashen duniya, su cimma matsaya guda da samun karin karfi daga annobar COVID-19, tare da kasancewa tsintsiya madaurinki daya, da nufin samar da kyakkywar makoma ga bil adama.

Wang Yi, ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da jawabi yayin wani taro na kwararrun kasa da kasa ta kafar intanet.

Da yake kira ga dukkan kasashen duniya su karfafa hadin kai domin cin nasara a yaki da COVID-19, ministan ya ce Sin za ta ci gaba da yayata gogewar da ta samu wajen dakile bazuwar annobar da dabarun jinya, da taimakawa kasashe da yankuna masu bukata da kuma cika alkawarinta na samar da riga kafin cutar ga duniya.

Ya ce akwai bukatar kasashe su inganta tsarin shugabanci na duniya ta hanyar karfafa huldar kasa da kasa, yana mai cewa, kasarsa za ta ci gaba da goyon baya da kuma kulla hulda da kasa da kasa bisa ka’idojin MDD.

Bugu da kari, Wang Yi ya ce kasashe na bukatar inganta farfado da tattalin arzikin duniya ta hanyar dunkulewa da kara bude kofa.

Ya ce yarjejeniyar hadin kan raya tattalin arziki ta RCEP da aka rattabawa hannu ‘yan kwanakin da suka gabata, ta alamta kafa wani babban yankin ciniki cikin ‘yanci mafi girma a duniya, yana mai cewa Sin za ta ci gaba da hada hannu da sauran kasashe wajen samar da hanyoyin saukaka zirga-zirgar mutane da hajoji da kuma daidaita tsarin samar da kayayyaki na duniya. (Fa’iza Mustapha)

 

 

 

 

 

 

Exit mobile version