Kasar Sin Tana Goyon Kiran Da Kasashe Masu Tasowa Ke Yi Na Kawar Da Sharadin ‘Yancin Mallakar Fasahar Riga Kafin COVID-19

Daga CRI Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, kasarsa ta fahimta sosai tare da goyon bayan kiraye-kirayen da kasashe masu tasowa suke yi, na neman cire sharadin ‘yancin mallakar fasaha game da riga kafin COVID-19.

Zhao Lijian, wanda ya bayyana haka Litinin nan, ya ce a matsayinta na babbar kasa mai tasowa, kana kasar dake sauke nauyin dake bisa wuyanta a duniya, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari a yaki da wannan annoba, tare da goyon bayan raba riga kafin bisa adalci tsakanin kasashe masu tasowa.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin kasashe masu tasowa, sun samu riga kafin cikin sauki da kuma rahusa, baya ga samarwa al’ummominta riga kafin masu yawa.

Ya bayyana cewa, kasar Sin ta samarwa sama da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 80 tallafin riga kafin. Ta kuma fitar da riga kafin zuwa sama da kasashe 50, kasar Sin ta kuma kulla yarjejeniya da sama da kasashe masu tasowa 10, ciki har da Masar, da hadaddiyar daular Larabawa a fannin fasaha da samar da alluran riga kafin a kasashensu.

Zhao ya kuma yi kira ga Karin kasashe, da su taimakawa kasashe masu tasowa, wajen ganin sun samu riga kafin, ta yadda za a yaki wannan annoba nan da nan. (Ibrahim)

Exit mobile version