CRI Hausa" />

Kasar Sin Tana Maraba Da Yadda Kafafen Yada Labarai Daga Kasashe Daban-daban Za Su Yada Labaran Wasannin Olympics Na Lokacin Sanyi

Kasar Sin ta bayyana cewa tana Maraba Da Yadda Kafafen Yada Labarai Daga Kasashe Daban-daban Za Su Yada Labaran Wasannin Olympics Na Lokacin Sanyi Da Na Nakasassu Na Beijing

A ranar Juma’a ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya bayyana cewa, kasarsa ta bukaci kasar Sin da kada ta takaita ‘yancin zirga-zirga ga ‘yan jaridu a lokacin wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, tare da tabbatar da kare lafiyarsu da ‘yancin bayar da rahotanni.
Da yake mayar da martani ga kalaman na Amurka Jumma’ar nan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, ‘yan jarida fiye da 2,500 ne suka mika takardar neman rajista don watsa rahotanni game da gasar Olympics ta lokacin sanyi ta birnin Beijing.
Wang Wenbin ya kara da cewa, kasar Sin tana maraba da ‘yan jaridu, da su rika ba da rahoto kan gine-ginen wuraren wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing, da shirye-shiryen gasar, da tabbacin gudanar da aiki da sauran ayyukan da ke da alaka da su, da kuma gudanar da aikin sa ido, wanda zai taimaka mana wajen inganta tsari da gudanar da ayyukanmu. Sai dai kuma, kasar Sin ta yi kakkausar suka ga yadda ake siyasantar da wasannin motsa jiki, da akidar nuna kyama ga kasar Sin, da kirkirar labarai da bayanan karya da ke bata sunan kasar Sin da wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing da sunan ‘yancin ‘yan jarida.

Exit mobile version