Kasar Sin Za Ta Gabatar Da Sabon Tsarin Gudanar Da Sufurin Jiragen Kasa A Watan Oktoba

Daga CRI Hausa,

Kasar Sin za ta aiwatar da wani sabon tsarin zirga-zirgar jiragen kasa daga ranar 11 ga watan Oktoban 2021, domin kara inganta sufurin jama’a da kayayyaki.
A cewar kamfanin kula da zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin, za a inganta hidimar jiragen jigilar kayayyaki tsakanin Sin da Turai, kuma a matsakaicin mataki a kowacce rana, jiragen jigilar kayayyaki 78 za su hada birane 174 dake kasashen Turai 23, adadin da ya karu da guda 5 a kan wanda ake da shi yanzu.

Haka kuma, sama da jiragen jigilar kayayyaki 21,000 ne za su rika bin layukan dogon kasar Sin a kowacce rana.
Baya ga haka, wasu layukan dogo da dama za su fara aiki a karshen bana, inda wasu birane za su samu layukan dogo a karon farko. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CRI Hausa)

Exit mobile version