Kasar Sin Za Ta Shirya Muhawar Bainar Jama’a A Kwamitin Sulhu Don Tattauna Yadda Za A Sake Gina Afirka Bayan Annobar COVID-19

Daga CRI Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, a matsayinta na shugabar karba-karba na kwamitin sulhun MDD na watan Mayu, kasar Sin za ta shirya muhawarar bainar jama’a, kan “bunkasa matakan sake gina nahiyar Afirka bayan annobar COVID-19 da magance tushen rikice-rikice”.

Zhao wanda ya sanar da haka a Larabar nan yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, ya kuma bayyana cewa, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ne, zai jagoranci taron, tare da gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.

Zhao Lijian ya ce, annobar da har yanzu ake fama da ita, ta haddasa mummunan tasiri a fannonin siyasa, tattalin arziki da ci gaban zamantakewa a kasashen Afirka, musamman yadda ta yi tasiri na matsakaici da dogon zango kan kasashen dake fama da tashin hankali.
Ya ce, a yayin da ake yaki da wannan annoba, har yanzu kasashen na Afirka na fama da jerin barazana da kalubale a fannin zaman lafiya da tsaro.

A saboda haka ne, yana da muhimmanci cewa, kasar Sin a matsayinta na shugabar karba-karba na kwamitin sulhu na watan Mayu, ta shirya muhawarar bainar jama’a. Kasar Sin tana fatan yin aiki da sauran kasashen duniya, ciki har da mambobin kwamitin sulhu, domin kara fahimtar tasirin da annobar ta yi a dukkan fannoni a nahiyar Afirka, da kuma tattauna yadda za a taimakawa kasashen na Afirka fita daga wannan annoba, da magance tushen rikice-rikice, da tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba mai dorewa. (Ibrahim)

Exit mobile version