Daga Abba Ibrahim Wada
A gasar neman tikitin shiga jerin kasashen da za su isa kasar Kamaru domin buga gasar cin kofin Nahiyar Afrika a shekara ta 2022, kungiyoyi 7 ne yanzu haka aka tabbatar da sun samu wannan dama bayan da a ranar Laraba aka buga wasanni daban-daban.
kasar Burkina Faso ta yi canzaras da Uganda yayin da Malawi ta doke kasar Sudan ta Kudu da ci daya mai ban haushi. Sai Rwanda ta lallasa tawagar ‘yan wasan kasar Mozambikue da ci daya mai ban haushi ya yinda Sudan ta doke Sao Tome Principe da ci biyu da nema.
Ita ma kasar Madagascar ba ta ji da dadi ba a fafatawa da ta yi da Habasha, wacce ta yi mata ruwan kwallaye da ci 4 da nema sai Guinee da ta doke tawagar kasar Mali da ci daya mai ban haushi.
Bayan wadanan wasanni na ranar laraba, kungiyoyi 7 ne yanzu suka samu tikitin zuwa kasar Kamaru daga cikin kungiyoyi 51 bayan da aka cire Chadi daga cikin wannan tafiya sakamakon dakatar da ita da aka yi.
kungiyoyin da suka samu tikitin zuwa gasar ta cin kofin nahiyar afrika sun hada da kasar Kamaru mai masaukin baki sai kuma kasar Senegal wadda ta buga wasan karshe a gasar da ta gabata sai kasar Algeria mai kare kambu sannan sai kasar Mali da Tunisia da Guinee da kuma Burkina Faso.
A jiya Alhamis kuwa kasar Comoros ta karbi bakuncin kasar Togo sai Afrika ta kudu wadda ta kece raini da kasar Ghana ya yinda tawagar ‘yan wasan kasar Kenya zasu kece raini data kasar Masar sai kuma yau juma’a, Niger zata kece raini da kasar Côte d’Iboire.
A gobe Asabar kuwa tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Najeriya ce za ta yi tattaki zuwa birnin Porto Nobo na Jamhuriyar Benin domin ta faffata da kungiyar kwallon kafar ta jamhuriyar Benin wasan da Nigeriya take fatan samun nasara domin samun tikitin gasar.