Connect with us

KIWON LAFIYA

Kasashen Duniya Na Bukatar Dala Bilyan 264 Domin Daukaka Rayuwar Mata

Published

on

Sakamakon binciken da majalisar dinkin duniya (UN) ta gudanar ya nuna cewar kasashen duniya suna bukatar a kalla  dala biliyan 264 don inganta rayuwar mata.

Majalisar dinkin duniya ta gabatar da shi wannan sakamako ne a taron inganta rayuwar mutane da samar da ci gaba na kasa da kasa da aka yi a kasar Kenya a shekarar data gabata.

A lissafe dais hi abin yake kasashen duniya za su kashe wadannan kudaden ne wajen inganta kiwon lafiyar mata musamman a wajen haihuwa hana yi wa ‘ya mace aure da wuri, hana cin zarafin mace da samar wa duk mata dabarun bada tazarar iyali ko kuma abin da aka fi sani da tazarar haihuwa

Sannan za a yi amfani da wani kaso cikin wadannan kudade wajen daukan kwararrun ma’aikata a asibitoci, siyo magunguna da sauran kayan aikin da za a bukata domin inganta rayuwar mata da gudanar da bincike.

Shugabar UNFPA Natalia Kanem ta bayyana cewar kasashen duniya masu yawa sun gano cewar cin zarafin mata, yawan mace-macen mata da kananan yara, ga kuma   tsananin talauci ne matsalolin da suka damu kasashe masu yawa a duniya musamman ma wadanda suke tasowa.

Ta bayyana cewar wasu kasashen duniyan ma har sun tsara hanyoyin kawar da su amma karancin kudade ya hana hakan tabbatuwa

“Binciken na ko kuma Hukumar kula ta yawan al’umma ta majalisar dinkin duniya UNFPA ta yi ya nuna cewar mata 800 ne suke mutuwa kulun a dalilin matsalolin da suka shafi daukan ciki da kuma haihuwa, mata sama da miliyan 230 na fama da karancin dabarun bada tazarar iyali ta zamani, kulun ana cin zarafin mace daya  daga cikin mata uku bugu da kari  kuma kullun ana yi wa ‘yan mata 33,000 auren dole a duniya.

Shugaban kungiyar ‘Abenir Health’ John Stober ya ce sa yara a makarantar boko da koya musu sana’o’in hannu zai taimaka wajen kawar da duk  wadannan matsalolin.

Babbar sakatariyar ma’aikatar aiyukkan kasashen waje ta kasar Kenya Kamau Macharia ta bayyana cewar amfani da wadannan kudade zai taimaka wajen rage yawan marayu da cutar da rayuwar mata a sanadiyar cin zarafinsu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: