Connect with us

KASASHEN WAJE

Kasashen Duniya Na Gaf Da Fadawa Rikicin Kasuwanci – Putin

Published

on

Shugaban Rasha Bladimir Putin, ya yi gargadin cewa kasashen duniya na gaf da faddawa cikin gagarumin rikicin kasuwanci, sakamakon irin matakan da gwamnatin Amurka ke dauka domin bai wa masana’antunta fifiko.

Shugaba Putin ya yi gargadin ne a gefen taron tattalin arziki da ke gudana a birnin St Petersburg a ranar Juma’a, inda ya ce matakan da Amurka ke dauka na neman haddasa tarnaki ga sha’anin kasuwanci tsakanin kasashen duniya.

Putin, bai fito fili karara ya ambaci sunan shugaban Amurka Donald Trump ba a kalaman nasa, sai dai ya ce abin da duniya ke bukata a wannan zamani shi ne karfafa ma’amala da jama’a a maimakon sa-in-sa.

Shugaban na Rasha dai ya bayyana matakan da Amurka ke dauka a fagen kasuwanci da cewa sun yi hannun riga da dokokin kasa da kasa, kafin daga bisani ya yi kakkausar suka a game da haraji da kuma takunkuman da Amurka ke sanya wa kamfanoni da kuma kasashen duniya a cikin ‘yan watannin baya bayan nan, ba tare da mutunta dokokin kasuwanci ba.

Akwai dai shugabannin kasashe da dama da ke halartar wannan taro na tattalin arziki a birnin St Petersburg, da suka hada Emmanuel Macron na Faransa da kuma Firaminista Shinzo Abe na Japan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: