Rabiu Ali Indabawa" />

Kasashen Indiya Da Pakistan Za Su Yi Atisayin Soja Na Hadin Gwiwa

Yanzu haka dai a wani mataki na ba saban ba ko kuma matakin da ba’a taba gani ba, kasashen yankin kudancin Asiya biyu masu karfin makaman nukiliya kasar India da Pakistan za su fara wani atisayen soja na hadin gwiwa.

A cikinmakon da ta gabata ne ministan tsaron India, Nirmala Sitharaman ya tabbatar da cewa India zata bi sahun atisayen yaki da da ‘yan taadda ita da kasar Pakistan.

Sai dai wannan shi ne karo na farko da za aga kasahen biyu da aka rabu tun a shekarar 1947, sun yarda da juna kuma harma zasu yi wani abu wuri guda karkashin kungiyar kasashen dake yankin Kudancin Asiya a karkashin kulawar Rasha kumaa cikin watan Agustta ne za ayi wannan atisayen

Ita dai wannan kungiyar ta tattalin arziki da tsaro da bunkasa demokaradiyya an samar da ita ce a Shanghai na kasar China a shekar 2011, kuma kasashen da suke cikin ta sun hada da China, India, Kazakhastan, Pakistan, Russia, Tajikistan sai kuma Uzbekistan.

Exit mobile version