Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Kasashen Sin Da Afirka Sun Zama ‘Yan Uwa Rabin Jiki

Published

on

Yanzu ya kara tabbata cewa, kasashen Sin da Afirka, sun zama abin da malam Bahaushe ke cewa, ‘yan uwa Rabin Jiki, domin a yayin da kasar Sin ke yaki da COVID-19, a daya hannun kuma kasashen Afirka sun nuna mata goyon baya, inda sama da shugabannin kasashen nahiyar 50 suka bayyana goyon baya da ma taimakonsu ta hanyar buga wayar tarho ko sanarwa ga shugabannin kasar Sin.
Dan Halak aka ce ba ya manta alheri, a yayin da cutar COVID-19 ta barke a nahiyar Afirka, kasar Sin ba ta manta da goyon baya da taimakon da ‘yar uwa kuma sahihiyar kawarta nahiyar Afirka ta ba ta ba, inda ita ma ta samar mata da taimako da tallafi da goyon baya ta fannoni daban-daban. Wadannan sun hada da tura kayayyaki da tawagar ma’aikatan lafiya na gaggawa zuwa kasashen Afirka, da shirya tarukan musayar dabaru ta kafar bidiyo da masanan lafiya da tarukan horaswa ga ma’aikatan lafiya a Afirka. Matakan na kasar Sin, sun taimakawa nahiyar matuka wajen yakar annobar yadda ya kamata. Na baya-bayan nan, shi ne taron kolin musamman na kasashen Sin da Afirka kan yaki da wannan annoba cikin hadin gwiwa da aka shirya ta kafar bidiyo, taron da kasashen Sin da Afirka ta kudu wadda ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka(AU) da kasar Senegal dake shugabancin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCAC) suka shirya cikin hadin gwiwa
A yayin taron kolin shugaba Xi ya yiwa nahiyar albishir a fannoni da dama, inda ya ce kasar Sin za ta soke bashin da take bin wasu gwamnatocin kasashen Afirka da babu kudin ruwa a cikinsu, wadanda ya kamata su biya a karshen shekarar 2020. Sannan, ga kasashen na Afirka da COVID-19 ta yiwa mummunar illa kana suke da matsalar kudi, kasar Sin za ta yi aiki da ragowar kasashen duniya, wajen ba su taimakon da ya dace, da kara musu wa’adin dakatar da biyan bashin, don taimaka musu fita daga wannan matsala. Haka kuma, Kasar Sin za ta yi aiki da sauran mambobin kungiyar G20, don aiwatar da shirin na DSSI, kuma bisa wannan tsari, Xi yana kira ga G20, da ta taimaka wajen dakatar da biyan bashin ga kasashen da wannan batu ya shafa, ciki har da wadanda ke Afirka.
Kasashen Afirka sun yaba da hangen nesa da matakan da kasar Sin ta dauka na adawa da siyasantar da COVID-19 da nuna wariya da ra’ayi na kashin kai. Har kullum kasar Sin tana martaba alheri da wasu suka yi mata na abota, kuma duk lokacin da abokai da ‘yan uwanta suna cikin bukata, ba za ta kawar da kai ba tare da yin wani abu a kai ba.
Shugaba Xi ya sake jaddada alakar Sin da Afirka, duk da yadda wasu kasashen duniya ke neman bata wannan dangantaka. Don haka ne ma, ya ce zai ci gaba da tuntubar shugabannin Afirka ta yadda za a gudu tare a tsira tare, sanin kowa ne cewa, duniya tana fuskantar sauye-sauyen da ba ta taba gani a cikin wannan karni ba. Duba da irin sabbin damammaki da kalubalen da duniya take fuskanta, akwai bukatar hadin gwiwar kut-da kut tsakanin Sin da Afirka, fiye da yadda ake da shi a baya.
Alakar Sin da Afirka a fannin yaki da COVID-19, wata manuniya ce, dake bayyana matsayin kasar Sin na bunkasa alakar kasa da kasa kan yaki da matsalar da duniya ke fuskanta. Abokantakar Sin da Afirka dai, ya kasance abin misali a alakar kasa da kasa da ma alakar kasashen masu tasowa.
Daga matakin taimakawa juna a gwagwarmayar kwatar ‘yanci da neman ci gaba tare kafada da kafada, Sin da Afirka sun cimma sakamako mai gamsarwa wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen su, da inganta rayuwar jama’arsu da kara jin muryar kasashe masu tasowa a dandalin kasa da kasa. Don haka, duk mai neman bata alakar sassan biyu, ba zai yi nasara ba. Duniya za ta ga bayan wannan annoba, kuma al’ummar Sin da Afirka na da yakinin ganin tarin alheri a nan gaba. (Ibrahim Yaya)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: