Kasashen Turai 3 Sun Roki Amurka Don Ceto Kamfanoninsu A Iran

A wata wasikar hadin gwiwa da ministocin kudi da na harakokin wajen kasashen Faransa, Jamus da Britaniya suka sanya wa hannu sun roki Amurka, kan ta tsame kamfanoninsu daga cikin sabbin takunkuman da ta sakawa kamfanonin da ke ci gaba da aiki a Iran. Wasikar mai dauke da kwana 4 ga wannan watan nan na Yuni, ga Sakataren wajen na Amurka Mike Pompeo da na baitil mali Steben Mnuchin, wadda ministan kudin Faransa Bruno Le Maireya ya wallafa a shafinsa na Twitter, ta nuna yadda ma’aikatun kudi dana harkokin wajen kasashen 3 ke neman Amurka ta dakatar da daukar mataki kan kamfanoninsu baya da suka ki amince wa da matakinta na ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.

A cewar Fransa Jamus da kuma Britaniya akwai bukatar Amurkan ta dakatar da daukar duk wani mataki da zai haifar da tarnaki ga muradu da kuma tsaron nahiyar Turai. A cikin wasikar ta hadin guiwa da ta samu saka hannun Shugabar ofishin kare manufofin ketare ta kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini, ta ce ko da kasar Amurka ta yanke hukuncin ficewa daga cikin yarjejeniyar nukliyar Iran, su a kullum sun yi amanar cewa yarjejeniyar ce hanya mafi dacewa wajen hana kasar Iran mallakar makaman Nukliya.

Moghereni ta ce a matsayinsu na kawaye ga Amurka suna fatan ganin sabbin takunkuman na ta kan Iran kada su shafi kamfanonin da alúmmar turai. Har ila yau kasashen 3 na fatan ganin Amruka ta mutunta matsayin siyasar da suka dauka, haka kuma daukacin ‘yan kasuwa da yan kwangilar halataciyar nahiyar ta turai, na rokon ganin Amruka ta janye kamfanoninsu da suka fara aiki a kasar ta Iran daga cikin takunkuman, domin samun damar kammala kwangilolin da suka kulla da kasar Iran tun bayan fara aikin da yarjejeniyar nukliyar ta 2015.

Exit mobile version