Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Kasashen Turai Sun Nuna Shakku Kan Dalilin Yunkurin Amurka Na Haramta Tik Tok

Published

on

Ranar 15 ga watan Satumba mai zuwa ta kasance rana ta karshe na wa’adin da shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya dibar wa manhajar Tik Tok, wato in dai ba a kai ga sayar da manhajar ba, lallai wannan manhajar da ke samun farin jini a fadin duniya zata fuskanci haramci a kasar ta Amurka. Sai dai matakin ya samu suka da shakku daga kasashen Turai game da dalilin da ya sa Amurkar daukar matakin.

Sakamakon matsi daga shugaba Trump, kamfanin ByteDance da ya mallaki manhajar ya fitar da sanarwar cewa, yana tunani kan sake kafa hedkwatar Tik Tok a wani birnin da ke wajen Amurka. A labarin da kafofin yada labarai na Burtaniya suka bayar, an ce birnin ka iya kasancewa London, kuma tuni gwamnatin Burtaniya ta amince da shirin.
A cewar kakakin gwamnatin Burtaniya, kasar za ta samar da budaddiyar kasuwa mai adalci ga jarin da aka samar da zai iya taimakawa bunkasuwar tattalin arziki da kuma samar da karin guraben aikin yi.
A hakika, shugaba Trump ya sanya haramci kan Tik Tok bisa dalilin “kiyaye tsaron kasa” ba tare da samar da shaidu kan ayyukan da Tik Tok din ya tafka na barazanar tsaron kasar ba, kuma bai yi karin haske a kan ta yaya manhajar za ta iya ci gaba da gudana ba. A maimakon haka, sai ya yi amfani da ikonsa yadda ya ga dama, ba tare da yin la’akari da ka’idojin kasuwanci ba, a yunkurinsa na lahanta kamfanonin kasar Sin.
Baya ga haka, shugaban ya bayyana a fili cewa, in dai an sayar da Tik Tok yadda ya kamata, to, ya kamata gwamnatin Amurka ta samu ladanta daga cinikin.
A wani sharhin da jaridar Frankfurter Rundschau ta gabatar, an ce wannan mataki mai “salon Trump”, wanda aka dauka bisa dalili mara tushe tare da manufar siyasa. A babban zaben da za a gudanar nan ba da jimawa ba, shugaban na fatan karkata hankalin masu zabe game da yadda bai dauki matakan da suka dace wajen shawo kan cutar Covid-19 ba.
A cikin ’yan shekaru kalilan, manhajar Tik Tok ya samu farin jini cikin sauri a fadin duniya, musamman a wajen matasa, wadanda suka nuna sha’awarsa fiye da Facebook da ma sauran kafofin sada zumunta. Ko a watan da ya gabata ma, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya saka hoton bidiyonsa na farko ta kafar, don taya ’yan makarantar sakandare murnar kammala karatunsu. To, a zahiri dai da wuya Amurka ta yi na’am da nasarar da manhajar ta samu.
A wurin Amurka, maganar “tsaron kasa”, hakika wani suna ne na “fin karfi”, kuma kasar ta sha yin amfani da dalilin wajen lahanta kamfanonin sauran kasashe, ciki har da kamfanin ALSTOM na Faransa da kuma Toshiba na Japan.
Mr. Frederic Pierucci, a littafin da ya rubuta mai suna LE PIEGE AMERICAIN, wani tsohon babban jami’in kamfanin ALSTOM, ya tona asirin gwamnatin Amurka game da yadda ta lahanta kamfanonin sauran kasashe bisa ga abin da ya faru gare shi.
Ya kuma bayyana wa manema labarai cewa, a hakika, Amurka ta saba yin amfani da dokokin kasar a matsayin makaminta na farwa wadanda take takara da su. Baya ga haka, ya yi kira ga kamfanonin kasar Sin da su kara kasancewa cikin shiri, tare da yin kira ga kasa da kasa da su hada kansu don tinkarar matakan da Amurka din ta dauka na nuna fin karfi. (Lubabatu Lei)
Advertisement

labarai