Sarkin Saudiyya ya nada dansa, Mohammed bin Salman a matsayin yarima mai jiran gado, bayan ya cire dan dan uwansa, Mohammed bin Nayef, daga matsayin.
Har ila yau sarki Salman ya ba da umarnin cewa dansa yarima Mohammed mai shekara 31, zai zama mataimakin Firai Minista, yayin da zai ci gaba da rike mukaminsa na ministan tsaro.
An cire yarima Mohammed bin Nayef, mai shekara 57 ne daga mukaminsa na shugaban tsaro na cikin gida, in ji kafafan yada labarai mallakar gwamnati.
Kamfanin dillancin labaran SPA ya ruwaito cewa Nayef ya yi mubaya’a ga sabon yarima mai jiran gadon.
Amma sanya yarima Mohammed a matsayin mai jiran gado zai sa matasan kasar su fara kallon cewa abubuwa na sauyawa.
kafin samun mukaminsa na baya-bayan nan, yariman ne ya jagoranci yakin Saudiyya a Yemen, yayin da yake lura da manufar masarautar kan makamashi da sauye-sauyen tattalin arziki.
Kafar Sadauwar BBC ta hakaito cewar, mai yiwuwa ne yariman ya bata wa wasu rai daga cikin ‘yan gidan sarauta wadanda suka saba da jagorancin tsofaffi.
Babansa, sarki Salman yana da shekaru 81, kuma rahotanni sun ce ba shi da cikakkiyar lafiya.
Mohammed bin Nayef zai iya shafe gommannin shekaru yana jagorancin kasar.
Ci gaban da yarima Mohammed bin Salman ya samu a fagen siyasa abu ne da ya faru cikin kankanin lokaci.
Duk da cewa yana matashi kuma bai yi wata gwagwarmaya a siyasance ba, amma yau yana gaf da rike mulkin kasa mafi karfi a yankin Larabawa.
Ya kori da yawa daga cikin ‘yan amshin shata daga aikin gwamanti, kuma ya maye gurbinsu da matasa masu ilimin boko. Ya kaddamar da wani shirin ci gaba mai suna “Bision2030”, kuma ya bayyana shirin sayar da wani bangare na katafaren kamfanin man kasar, Aramco.
Ya kuma kulla alaka da Washington da kuma gwamantin Trump.
Amma mataki mafi hatsari ka iya zama kokarinsa na rage ikon malaman addini masu ra’yin ‘yan mazan jiya. Washington tana son wannan yunkurin, amma wasu a cikin gida ba sa son hakan.
Mutumin da ya assasa masarautar, Sarki Abdulaziz (da aka fi sani da Ibn Saud), ya haifi ‘ya’ya da yawa, kuma ‘yan gidan sarautar kasar sun kai 15,000.
A shekarar 2006, an ayyana wata doka wadda ta nada wani kwamiti da ke da alhakin zaben sarki da yarima mai jiran gado.
Kwamitin ya kunshi manyan mazaje ‘yan gidan sarautan Al-Saud, kuma an fi sanin kwamitin ne da sunan majalisar mubaya’a.