Kwanaki kadan kafin karamar Sallah, ‘yan kasuwa da jama’ar gari duka suna kukan rashin kudi. A gefe daya, jama’a suna cewa kayan abinci da na sutura duk sun yi tsada.
Wasu mata da suka je kasuwa sun zanta da manema labarai, inda suka bayyana cewa lamarin tsadar kaya sai dai a rufe baki kawai. Wata mata, Malama Fatsuma, ta ce jama’a suna da kudi, sai dai kayayyaki ne suka yi tsada. Amma wani malamin cewa ya yi gaskiyar magana ita ce, babu kudi a hannun mutane.
Su ma wasu ‘yan kasuwa Abubakar da Habu, suna cewa su dai hali irin na bana daban yake. Suka ce, mutane za su je rumfunansu su tambayi farashin kaya, amma maimakon su saya, sai su ce sai sun dawo.
Wannan matsala tana da nasaba da matsalolin faduwar farashin man fetur, da kuma na wasu ma’adinai kamar Uranium a kasuwannin duniya ba.