Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KASASHEN WAJE

Kashe Fararen Hula Na Karuwa A Iraki Da Syria

by Tayo Adelaja
September 17, 2017
in KASASHEN WAJE
1 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Wata Kungiya da ke sa’ido kan rikice-rikice a duniya ta ce hare-haren da jiragen yakin kawance karkashin jagoranci Amurka ke kai wa Iraki da Syria ya lankwame rayukan fararen hula sama da 700. Rahotan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Kungiyar Amnesty international ta bukaci a aiwatar da bincike kan kisan fararen hula, a lokacin da aka yi kokarin kwato birnin Mosul na Iraki. Kungiyar Airwars da ke zaman kanta, ta ‘yan jaridu da masu bincike da ke amfani da kafafan sada zumuta da shaidun gani da ido, wajen tattara bayananta, ta ce fafatawar da akeyi da mayakan jihadi a Raka na Syria da Mosul da ke Iraki ya munana. Kuma alkaluman da ta fitar ya sha ban-ban dana Amurka, da ke cewa fararen hula 603 ta kashe a bisa kuskure tun kaddamar da yakin rundunar kawance karkashin jagorancinta a 2014. Daraktan Kungiyar ta Airwars, Chris wood, ya ce karuwar hare-haren kwato Mosul da Raka ya rubanya alkaluman fararen hula da suka kwanta dama, inda ya ce muradun Pentagon na kawar da mayakan jihadi ya jefa rayuwar fararen hula a cikin hatsari. Kungiyar ta ce tsakanin fararen hula 529-744 aka kashe a watan Yuni, karin sama da kashi 50 na watannin baya. A ranar talatar da ta gabata Amnesty ta bukaci a gudanar da bincike a Mosul kan kisan fararen hula, inda ta zargi dakarun Iraki da gaza kare rayukan al’umma. Sai dai Laftanar janar Stephen Townsend da ke jogoranci rundunar kawance yakar IS ya yi watsi da zargin.

SendShareTweetShare
Previous Post

Jami’an Tsaro Su Na Halaka ’Yan Gudun Hijira A Congo

Next Post

’Yan Awaren Kataloniya Sun Yi Nasara

RelatedPosts

Faduwar Trump

Me Zai Biyo Bayan Darewar Karajar Biden Da Faduwar Trump?

by Muhammad
7 days ago
0

Idanun duniya na kan ranar Larabar jiya, 20 ga Janarairu,...

Rigakafi

An Soma Yin Allurar Korona A India Da Brazil

by Muhammad
7 days ago
0

A yau asabar kasashen Duniya da suka hada Indiya ,Brazil...

Trump Ya Fice Daga Fadar ‘White House’ Gabanin Rantsar Da Biden

Trump Ya Fice Daga Fadar ‘White House’ Gabanin Rantsar Da Biden

by Muhammad
1 week ago
0

Trump ya ce mutane "ba su san aiki tukuru" da...

Next Post

’Yan Awaren Kataloniya Sun Yi Nasara

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version