Kashe-Kashe Mutane A Katsina: Maganar Ciki…

Batun kashe-kashen jama’a da ya zama ruwan dare gama duniya a yankin arewa musamman jihar Katsina wato jihar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya ta’azza inda yanzu ta kai wani matsayi wanda sai dai a ce Innalillahi Wa inna Ilahi Raji’un.

Abubuwa da suke daurewa jama’a kai shi ne yadda wannan lamari kullin sai cigaba yake kamar wutar daji inda har yanzu an kasa kawo karshen wannan matsala duba da irin matakan da gwamnati a matakin jiha da kuma tarayya suke cewa suna dauka amma dai kamar jiya kamar yau.

Akan haka jama’a da dama suna hasashe da nuna shakku game rashin karewar wannan matsala, wasu suna cewa ba a dauki matakin da ya kamata ba ne wasu kuma suna cewa akwai sa hannun masu rika da madafun iko acikin lamarin.

Koma dai ya ya aka yi? Wannan matsala babba ce kuma tana kawo koma baya a dukkanin al’amuran da suka shafi jama’a na yau kullin musamman tattalin arziki da Ilimi da Noma da walwalar jama’a da sauran abubuwa.

Wadanda wannan matsala ta shafa kai tsaye kulin da sabon bayanin da su ke yi, duk lokacin da suka ji wani motsi daga gwamnatin musamman ta tarayya sai sun furta wani abu sabanin abinda gwamnati ta ce wanda haka kullin yana kara fitowa da wasu abubuwa fili.

Idan muka koma baya, mun sha jin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya wasa da duk wani hakki ko bukatar da ta shafi harkar tsaro idan har batun ya kai a gaban ofis dinshi, idan kuwa haka ne to a ina matsalar ta ke?

Wannan ita ce tambayar da kwanan nan muka fara jin amsarta daga wani jigo a gwamnatin jihar Katsina wanda ya sha ta dubu ya fadi daya daga cikin abubuwan da mutanen da wannan bala’I ya shafa su ke yawan ambatawa amma har yanzu maganar ba ta kai kunnen shugaban kasa ba.

Jihar Katsina ta koma kamar Siriya ta yadda kullin sai an kai hari, sai an kashe mutane sai an lalata dukiyoyinsu ba adadi duk da cewa akwai jami’an tsaro da su ke aikin samar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

A matakin jihar gwamnatin jihar Katsina ta sha fada cewa duk abinda jami’an tsaro suke bukata da za su yi wannan yaki a bangaranta ta samar da shi, abinda kaiwa ya rage shi ne neman sa’a da kuma nasara.

Wani abun mamaki duk da cewa akwai wadannan jami’an tsaro da aka samar domin yin wannan aikin na musamman kukan da jama’a ke yi shi ne idan suka kai rahoto ga jami’an tsaro cewa ga ‘yan bindiga nan za su kawo masu hari babu wanda ke kula da wannan bukata ta su, idan ma abin ya ci tura sai dai ka ji sun ce sojojin da aka kai wajan sun ce ba a ba su ikon motsawa daga inda suke ba.

Duk da cewa a na ba su wasu kudadai na musamman da ake zargin cewa manyan su ne suke yin  rub-da-ciki da kudadan, wani lokaci kuma sai bayan an gama kai hare-haran sannan sai a gan su suna borin kunya bayan an kashe jama’a da lalata dukiyoyinsu.

Ganin yadda wannan lamari ke cigaba da faruwa tasa hatta su kansu jami’an gwamnatin jihar Katsina sun fara karatun ta nustu, sun kuma fara ankara daga zargin da mutanen kauye ke yi na cewa Sojojin nan fa da aka kai sun koma kamar hoto babu abinda suke illa cin kudin jama’a.

A wata hira da manema labarai suka yi da sakataren Gwamnatin jihar Katsina Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa ya bayyana masu cewa sojoji basu aikin da ya kamata domin dakile ‘yan ta’adda.

Haka kuman an rawaito sakataren gwamnatin yana bayyana wa manema labaran cewa, wani hari da aka kai a ranar lahadi a wani kauye wanda bai fi nisan kilomita biyu zuwa uku ba daga sansanin da sojojin suke ba, wanda yawan su ya kai kimanin 360, amma ba abinda suka yi, da aka tuntube su sai suka ce ba su da wadatattun kayan aikin da za su iya tunkarar maharan.

Ya kara da cewa sati biyu zuwa uku da suka gabata ya yi magana da Birgediya kan wannan matsalar kuma ya san cewa gwamnatin jihar Katsina ta yi duk wani abu da ya kamata kan sojojin, amma sai suka nuna ba su da kayan aikin da zasu iya tunkarar maharan.

A cewarsa sun karaya kan yadda sojojin ke gudanar da ayyukan su, inda ya bayyana cewa ‘yan sanda sun yi bakin kokarin su musamman ma a wannan gwamnatin.

Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ya bayyana cewa gwamantin jihar Katsina ta yi duk abin da ya dace ga sojojin, domin suna jin ciwon irin yadda mutanen ke ganin gwamnati bata yin kome kan wannan lamari. Ya ce basu da hurumin ba sojojin umurni aikin su kawai su taimaka masu da kayan aikin da zasu taimaka wa sojojin domin su yaki ‘yan ta’addar.

Kazalika ya bayyana cewa idan har gwamnatin tarayya na son magance wannan matsalar to akwai bukatar a hada wata gagarumar runduna wadda ta hada da sojoji da ‘yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya da duk wasu wadanda ke da ruwa da tsaki a bangaran tsaro. 

A bangaran su kuma suna da mutane wadanda suka san dajin nan da yadda yake wadanda zasu taimaka wa jami’an tsaron wajen magance matsalar, kuma irin wannan rundunar a same ta a jihohin Kaduna da Zamfara da Katsina da Naija kuma su fara aiki lokaci guda domin kawo karshen barazanar ‘yan bindiga a wadannan yankuna. 

Ya tabbatar da cewa in aka yi haka ba za a dauki sati 46 ba sai matsalar ta zama tarihi a wannan yankin da kuma jihar Katsina inda nan yanzu wannan iftila’I ke faruwa ba dare ba rana.

Sai dai kuma a bangaran jami’an tsaron an tuntubi Kwamanda na 17 Birget Birgediya Janaral Lukuman Amunoyi, kan wannan korafi da Sakataren gwamnatin jihar Katsina ya yi game da aikin sojojin a jihar Katsina, inda ya bayyana cewa sojojin suna yin bakin kokarinsu wajen ganin sun magance wannan matsala ba tare da wani tsaiko ba.

Ya kara da cewa aikin na su yana da iyaka, kuma sannan suna bukatar kayan aiki da zasu taimaka wajen magance wannan matsala. Daga karshe ya yi kira da cewa nan ba da dadewa ba zasu kawo karshen wannan matsala. 

A cewarsa yanzu abinda kawai suke  bukata shi ne a basu goyan bayan da hadin kai wajen Magance wannan Matsala wanda suma kansu abin ya fara isar su ganin irin asarar rayuka da dukiyoyi da ake yi kullin ba dare ba rana.

Yanzu idan muka duba wadannan kalamai na sakataran gwamnatin jihar Katsina akan wannan matsala muna iya cewa su a bangaran gwamnatin jihar Katsina suna iyakar kokarinsu wajan ganin wannan matsala ta zo karshe.

Sai dai kash! Ga alama kamar su bangaran tsaron ba su shirya ba tunda har gobe baban korafinsu shi ne ba su da kayan aiki, kuma wannan yaki yana bukatar kayan aikin fiye da kima sannan gwamnatin tarayya ce ke da alhakin samar da wadannan kayan aikin da suke magana a kai. 

Yanzu alamu na nuni da cewa idan har ba a samar da kayan aikin ba sai dai a karar da al’umar jihar Katsina jihar da shugaban kasa ya fito ke nan? Ko kuwa za samar da su amma ba a san lokaci ba, duba da cewa kullin sai an kashe jama’a sai an kone dukiyoyinsu a wannan yankuna da abin ya shafa.

Kiraye-kiraye da addu’o’I da al’ummomi suke yi ba dare ba rana, Allah buwayi gagara misali ya fara amsawa domin kuwa ko ba komi wannan magana da Sakataran gwamnati ya yi maganar ciki ce wanda nan gaba Insha’Allahu zata fito fili, wasu maganganun ma ai ba su faduwa a irin wannan muhali da an ji su, amma dai idan kere na yawo zabo na yawa…

Exit mobile version