Kashe-Kashe: Sifeton ’Yan Sanda Ya Yi Wa Zamfara Dirar Mikiya

Daga Hussaini Baba, Gusau

Shugaban ’yansanda na Kasa,Ibrahim K. Idris ya yi wa jihar Zamfara diyar mikiya dan daukar  matakin gaggwa ga maharan da suka addabi jihar ta Zamfara. Sifeton  ‘Yansandan ya bayyana cewa, Rundunar ‘yansanda ta yi shiri na musamman da sanya kwamiti mai karfin dan gano yadda al’amarin ke faruwa dan daukar matakin gaggwa. A fadar Mai martaba Sakin Zamfaran Zurmi, Alhaji Atiku Abubakar Muhammad, kuma ya jajanta ma wadanda suka rasa rayukansu da ke garin Birane da ke cikin Karamar Hukumar Zurmi.

Ibrahim K.Idris ya kuma bayyana wa Mataimakin Gwamnan Zamfara, Malam Ibrahim Wakala Liman cewa,’ za su samar da Runduna uku ta ‘yansandan Kwantar da tarzoma a Jihar ta Zamfara. Kuma  ya jajanta wa Mataimakin Gwamnan a gidan gwamnati da ya kai masa ziyara.

A nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Zamfaran Zurmi Alhaji Atiku Abubakar Muhammad, ya bayyana cewa, wannan hare-haren da aka kai akwai Sakaci na Jami’an tsaro dan tun kafin maharan su afka wa al’umma sai da na sheda wa Gwamna Abdua’ziz Abubakar Yari, Shi kuma Ya sheda wa Jami’an tsaro Babu wani mataki da su ka dauka dan haka idan Dansanda mai bindiga da Soja za su gaza tunkarar Maharan wane mutum ne zai iya tunkarar su?

Mai martaba Sakin Zamfaran Zurmi ya naimi shawara a kan a yi wa Jami’an tsaro Jihar Zamfara Kwaskarima  Kuma gwamnati ta ba su isasun kayan aiki da za su iya tunkarar kowace Rundunar mahara dan su maharan suna bisa mashina ya fi dari kuma kowane na dauke da Manyan bindigogi da mutum biyu a kan mashin din.dan haka ya zama wajinbi idan gwamnati da gaske take ta ba Jami’an tsaro kayan aiki na zamani.

Basarake ya kuma kara da cewa, su kam ba jaje suke bukata ba daga gwamnati “abun da muke bukata shi ne kare rayukanmu da dokiyoyinmu”.

Mataimakin Gwamna Malam Ibrahim Wakala, ya bayyana cewa, Godiyarsa ga sufeton ‘yansanda da ya kawo ziyar jaje ga al’ummar jihar Zamfara. kuma ya kuma bayyana cewa kwamitin da Sufeton zai sanya Allah ya sa ya zamo da mai ido dan a shekara ta 2014, sanda aka kai harin a Kauyan Kizar da ligyado gwamnati tarayya ta sanya kwamitin kuma har da manya Sojoji a ciki amma haryau bamuji sakamakon kaamitin ba.fatarmu shi ne kada ya zama irin wacan.kuma muna godiya da karin Runduna uku ta ‘yansandan Kwantar da tarzoma da za a samu kara mana.

Malam Wakala ya kuma jaddada cewa duk taimakon da ya kamata mu ba Jami’an tsaro za mu ba su fiye da yadda mUke badawa fatanmu shi ne kare Rayukan al’uMmar jihar Zamfara da dukiyoyinsu.

 

Exit mobile version