Daga Rabiu Ali Indabawa
Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya yi Allah wadai da kakkausan lafazi kan kisan da aka yi wa manoma shinkafa “kimanin 50” a garin Zabarmari, na Jihar Borno, da maharan Boko Haram suka yi. Gbajabiamila, wanda ya nuna bakin ciki game da kisan manoman, ya ce lamarin ya sake nuna bukatar sake daukar matakin soja a kan ‘yan ta’adda.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Lanre Lasisi, ya fitar a ranar Lahadi, mai taken, ‘Gbajabiamila ya yi tir da kisan manoman shinkafar Borno. Ya yi kira da a kara daukar matakan soja a kan masu tayar da kayar baya.’ Shugaban majalisar ya ce abin takaici ne. cewa “kusan 50 daga cikin manoman an kashe su ta mummunar hanya” a lokacin da kasar ke mai da hankali kan wadatar kai a fannin noman shinkafa.
Gbajabiamila ya jajantawa iyalan manoman da aka kashe da kuma mutane da Gwamnatin Jihar Borno kan wannan abin bakin ciki. Shugaban majalisar ya ce majalisar a shirye ta ke kuma ta bayar da dukkan goyon bayan da ya kamata, gami da tsarin kasafin kudi da ke gudana don tabbatar da cewa an kasafta kudade ga hukumomin tsaro don aiwatar da ayyukansu na kawar da ‘yan ta’adda.
“Bai kamata rayuwarsu ta tafi a banza ba. Wannan ya kamata a nemi karin mataki daga sojojin mu. A matsayin mu na Gida, a shirye muke ko yaushe mu basu dukkan goyon bayan da ya kamata, musamman ta hanyar kasafta kasafin kudi, don magance matattarar maharan. Ina tausaya wa iyalan manoman da aka kashe. ” A ranar Asabar ne kungiyar ta Boko Haram ta kashe manoman shinkafar a wani kauye da ke kusa da Maiduguri, wata al’umma ce da ke noma a Karamar Hukumar Jere, wacce ta shahara wajen noman shinkafa da sarrafa ta. An ba da rahoton cewa ‘yan ta’addar sun fara daure manoman ne, wadanda ke aiki a gonakin shinkafa, kafin su tsattsage makogwaronsu.