Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KASASHEN WAJE

An Kashe Masu Zanga-zanga 30 A Kenya

by Tayo Adelaja
October 18, 2017
in KASASHEN WAJE
1 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’ Adam ta Human Rights Watch da kuma Amnesty International, sun ce ‘yan sandan ƙasar Kenya sun hallaka a ƙalla mutane 33, yayin ƙoƙarin murƙushe masu zanga-zanga. Zanga-zangar ta ɓarke ne tun bayan sanar da nasarar shugaba mai ci Uhuru Kenyatta, wanda daga bisani kotun ƙolin ƙasar ta soke.

Sai dai janyewar jagoran ‘yan adawa Raila Odinga daga sake sabon zaɓen a wannan wata, ya sake rura wutar zanga-zangar. Aƙalla dai mutum 30 ake zargin ‘yan sanda suka kashe a yayin gudanar da zanga-zanga da ‘yan adawa suka yi a birnin Nairobi na ƙasar Kenya.

A wani sabon rahoton da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta fitar ta ce, ‘yan sandan ƙasar ‘’suna da hannu dumu-dumu’’. Har ila yau, akwai waɗansu rahotanni da ba a tabbatar ba, wadanda suke cewa ‘yan sandan sun kashe waɗansu mutum 17 a birnin.

Suna zargin ‘yan sandan da tayar da zaune tsaye ta amfani da ƙarfin da ya wuce kima a yankunan da ake tunani cewa ana tashin hankali. Ƙungiyar ta ce ‘yan sandan sun yi amfani da karfin da ya wuce kima ne a wuraren da ake zaton rikicin.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Kamaru Za Ta Tattauna Da Shugabannin Yankin Bamenda

Next Post

Mata Na Cikin Haɗari A Masar

RelatedPosts

Ebola

WHO Ta Aike Da Tawaga Ta Musamman Guinea Da Kwango Don Yaki Da Ebola

by Muhammad
1 week ago
0

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta sanar da daukar tsauraran...

Somaliya

Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci A Gaggauta Gudanar Da Zabe A Somaliya

by Muhammad
1 week ago
0

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bangarorin siyasar kasar Somalia da...

Alkalai

Alkalai Nijer Sun Gargadi ‘Yan Siyasa Su Daina Anfani Da Kalaman Kabilanci

by Muhammad
2 weeks ago
0

Alkali mai kare muradun hukuma (Procureur de la Republikue) ya...

Next Post

Mata Na Cikin Haɗari A Masar

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version