An Kashe Mutane Tara Da Garkuwa Da Wasu Bakwai A Adamawa

Mijiyoyin jami’an tsaron ‘yan sanda sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane tara da garkuwa da wasu yara kanana bakwai a wani kauyen da’ake kira Iware da ke kan hanyay Fofure- Jada a jihar Adamawa.

Haka kuma wata majiyar ta daban ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun shiga kauyen ne cikin dare inda suka kashe daukacin mutanen tara ‘yan gida daya.

“bayan kisan sun kuma tafi da yara bakwai, yanzu kuma suna neman kudin fansa” inji majiyar

“abin ya faru ne a wani sabon garin Fulani makiyaya da’ake kira Iware kusa da Beti Berre tsakanin yankin kananan hukumomin Fufore da Jada, masu garkuwar suna tsakanin Duwatsun yankin.

“a wannan yankin akwai masu garkuwa da mutane da dama akan Duwatsu, mafi yawan lokaci suna neman kudade ne a hanun wadannan da suke da Shanu.

“ jama’a suka sanar damu, kuma yanzu muna cikin shiri mu da sauran maharba, a shirye muke mu daukin wargaza matakin masu garkuwar” inji majiyar.

Da yake tabbatar da wannan batu jami’in Hulda da jama’a na rundunar’yan sandan jihar SP Othman Abubakar, yace tuni jami’an tsaro sun dauki mataki a kai.

“mun samu labarin faruwar wannan al’amari, amma har yanzu bamu da cikakken bayani akwai, tunda mun sani, muna sanar da jama’a game da ayyukan masu garkuwa da mutane a yanzu haka.

“kafin wannan lokaci, garkuwa da mutane yana can Dutsin Toungo, amma gashi kuma yanzu a Jada da Fufore” inji jami’in.

Rahotanni dai sunce masu garkuwa da mutanen sun kuma yi garkuwa da wani babban dan siyasa da kuma mamba dake wakiltar karamar hukumar Toungo a majalisar dokokin jihar a kwanan baya.

Haka kuma a baya an taba garkuwa da Sani Ribadu, dan uwa ga Malam Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC da Wilson Gundiri, kani ga Markus Gundiri, tsohon dan takaran gwamna a jam’iyyar SDP, yanzu kuma jigo a APC a jihar, sai an sake daga baya.

Exit mobile version