An Kashe Mutum 33 A Sabon Rikicin Kudancin Kaduna

Bayan wani sabon rikici da ya barke a ranar Lahadi da Litinin da ta gabata a yankin karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna tsakanin manoma da Fulani makiyaya.

Hukumar ‘yan sandan Jihar Kaduna a yau  ta tabbar da kisan mutum 33 bayan barkewar rikicin kamar yadda hukumar ta sanar.

Jami’an tsaron sun ce, an kashe Fulani 27 tare da wasu mutum shida mazauna yankin, yayin da wasu su ka jikkata lokacin rikicin.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna Agyole Abeh, ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma bayyanawa manema labarai cewa, a yanzu haka dai rikicin ya lafa sakamakon jami’an tsaro da gwamnatin jihar ta tura yankin.

 

Exit mobile version