Daga Abubakar Abba
Rundunar ‘yan Sanda ta jihar Enugu ta fara gudnar da binciken zarginda ake na kashe wani mutum akan sace Doya ɗaya a ƙauyen Amorji Nike dake Abakpa a cikin Jihar.
Kakakin rundunar, SP Ebere Amaraizu ne bayyana hakan a wata takarda ta rundunar ta fitar a jihar, inda takardar tace, abin ya auku ne ranar Huɗu ga watan Okutaba.
Kakakin ya ce, abin ya auku ne a ƙauyen Amorji Nike dake Abakpa dake cikin ƙaramar hukumar Enugu ta Yamma dake cikin jihar.
Kakakin ya ce, an yardar da Gawar mamacin a harabar da aka kashe shi.
A cewar kakakin, rundunar tana kan gudanar da bincike, akan lamarin, inda ya ce a halin yanzu, an cafko mutum biyu da ake zargi da aikat kisan.
Kakakin ya ce, waɗanda aka kama ɗin suna baiwa rundunar haɗin kai wajen gudanar da binciken.