Kashe Sojoji 70 A Nijar: An Soke Bukukuwan Ranar ‘Yancin Kai

Shugaban jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issofou ya sanar da soke duk wasu bukukuwan cikar kasar shekara 59 da samun ‘yan cin kai da aka shirya gudanarwa a ranar 18 ga watan Disamba a jihar Tillabery da ke Yammacin kasar da kuma ke iyaka da kasar Mali,sakamakon harin da kungiyar IS ta kai kan sansanin sojojin kasar.

Wannan wani mataki ne da shugaban ya dauka don nuna alhinin rashin sojojin kasar ta Nijar akalla 100 da kungiyar ta IS ta ce ta kashe a harin data kai kusa da iyakar kasar da Mali.

Bayanai na nuna cewa ranar Juma’a za ayi jana’izar sojojin da suka mutu bayan da gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na tsawon kwana uku a fadin kasar baki daya, tare da gudanar da addu’o’i ga wadanda suka mutun.

Harin dai shine mafi muni da aka kai kusa da iyakar kasar da Mali tun farkon rikicin Boko Haram a shekarar 2015.

Ita ma majalisar dokokin kasar cikin wata sanarwa ta yi tur da harin inda tayi fatan samun zaman lafiya mai dorewa a kasar ta Nijar.

Daya daga cikin ‘yan majalisar kasar, Mahamadou Daidouka ya ce majalisar ta mika sakon ta’aziyya ga ‘yan uwan dakarun da suka mutu da daukacin ‘yan Nijar baki daya ,sannan kuma a cewar shi, majalisar ta yi addu’ar Allah ya sauki ga sojojin da suka jikkata a harin.

Shi kuwa dan majalisa, Lamido Hamidou Moumouni ya bayyana bukata ga ‘yan kasa ta su yi watsi da banbance-banbancen dake tsakaninsu domin tunkarar ta’addancin dake barazana ga rayuwarsu.

Ya bayyana cewa kamata ya yi kowa ya tashi ya bada tasa gudummawar domin kare kasar daga rikicin masu tada-kayar-baya.

A baya-bayan nan dai, kungiyar IS ta kashe fiye da mutum 230 a Nijar da Mali da kuma Burkina Faso.

Exit mobile version