Connect with us

LABARAI

Kashi 10 Na ’Yan Nijeriya Na Zukar Wiwi

Published

on

Kungiyar ma’aikatan Asibitoci da masu harhada magunguna ta Nijeriya ta ce a halin yanzu zukar tabar Wiwi ce barazana mafi hadarin da aka fi da aikatawa a kasar nan, inda kungiyar ta kiyasta akalla kashi 10.8 na jimillan al’ummar kasar duk sun zuki tabar ta Wiwi a shekarar 2019.

Reshen kungiyar da ke babban birnin tarayya Abuja ne ya fadi hakan a ranar Juma’a, kungiyar ta ce akalla mutum guda daga cikin dukkanin mutane biyar da suka yi amfani da wani abu mai sa maye a yanzun haka yana fama da matsalar tabin hankali.

Shugaban kungiyar ta AHAPN na reshen Abuja, Abubakar Danraka, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar domin bukin ranar yaki da sha da kuma safarar miyagun kwayoyi a Duniya ta wannan shekarar ta 2020, ranar ta wannan shekarar wacce aka yi mata take da, ‘Better Knowledge for Better Care’.

Ya ce a Nijeriya, “Ofishin yaki da shan miyagun kwayoyi na majalisar dinkin Duniya, a shekarar 2018 ya bayar da rahoton cewa, kowane daya daga cikin ‘yan Nijeriya Bakwai da su ke a tsakanin shekaru 15 zuwa shekarun haihuwa 64 ya taba yin amfani da wani abu mai sanya maye wanda kuma ba taba ce ko kuma giya ba, ba kuma wai domin yin wani magani ba a shekarar 2017.

“Mutum guda daga cikin mutane biyar da suka yi amfani da kwayoyin da suke haddasa maye a shekarar da ta gabata su na fama da cutar tabin hankali a yanzun haka. Sannan kuma zukar tabar Wiwi ce annobar da aka fi da aikatawa a wajen shan abin da ke sanya mayen, an kiyasta akalla kashi 10.8 na jimillan al’ummar Nijeriya sun zuki tabar ta Wiwi a shekarar 2019. ‘yan Shekaru 19 da haihuwa ne suka fi zukar tabar ta Wiwi.

“Mu na yin amfani da wannan kafar wajen kara yin kira ga al’ummar Nijeriya da su hada hannu da masu harhada magunguna na kasar nan da saura kwararru a fannin lafiya domin wayar da kan al’umma a kan hadarin da ke cikin shan miyagun kwayoyi.

“Mu na kuma yin kira ga Iyaye da masu hakkin kula da yara da su bayar da lokutansu wajen kulawa da yaran da ke gabansu su ba su tarbiya tagari domin raba su da duk wata dabi’ar banza da kawar da hankulansu a kan duk wani abin da zai iya jefa su shan ababen da ke haddasa maye ta hanyar shan miyagun kwayoyi a gida da makarantu.
Advertisement

labarai