Connect with us

LABARAI

Kashi 43 Na ‘Yan Basa Hulda Da Hanyoyin Safarar Kudi Na Zamani

Published

on

Makarantar koyon ilimin kasuwanci dake jaharLegas, ta sanar da cewar, kashi 43 na ‘yan Najeriya basa yin hulda da hanyoyin sarrafa kudi na zamani. Bayanin hakan yana a kunshe a cikin rahoton kudi da makarantar da aka kaddamar a ranar alhamis a jahar Legas, inda makarantar ta kara da cewar, kashi 49 bisa dari na ‘yan kasar ne kacal suke yiun amfani da asusun ajiya na bankuna.Ta sanar da cewar, kashi takwas na ‘yan kasar ne kawai suke yin hulda da hanyar sarrafa kudi ta zamni, inda kuma kashi 36 bisa dari, suke yin amfani da hanayar sarrafa kudi na gargajiya. Da take yin tsokacin akan binciken Daraktan ilimi na makarantar Dakta Olayinka Dabid-West, waddda kuma itace take jagorantar hanyar sarrfa kudin na zamani na makarantar tace, wannan ya nuna cewar Najeriya bata shirya cimma burin ta na hulda da hanyar sarrafa kudi na zamani nan da shekara 2020 ba. A bisa binciken da makarantar ta yi, ya nuna cewar yin amfani da hanyoyin na hulda da kudi na zamani zai taimakawa Najeriya akan hada-hadar ta kudi. Ta yi nuni da cewar, rkarancin ilimi yana daya daga cikin kalubalen da ake fuskanta akan hanyar hulda da kudin ta zamani. Acewar ta, hakan ya janyo samun karancin gano abinda abokan hudda suke bukata ta kara da cewar, rahoton ya kuma bayar da alkibla akan irin halaiyyar alumma da aka kiyasta tra kai kashi 75 bisa dari na yawan alumomin kasar nan. Ta sanar da cewar, akwai bukatar mu gusa akan yadda zamu dinga yin hulda da abokan hada-hada yadda za’a inganta rayuwar su. Itama wata abokiyar a cikin hadaka kuma Darakta a Najejriya Dalberg, Nneka Eze ta ce, an gudanar da binciken ne Najeriya da kuma a kasashe biyar.Acewar ta, sanya fannin na kudi yafi karfin maganar bude asusu a bankuna.
Shirin na makarantar zai kuma ci gaba da gudanar da bincike akan hanyoyin hulda da kudi na zamani don a samu a cimma muradun karnin da aka sanya a gaba.
Advertisement

labarai