Abubakar Abba" />

Kashi 59. 7 Hukumar FIRS Ta Tura Wa Matakan Gwamnati Uku A Wata Uku – RMAFC

Shugaban hukumar tara kudade ta tarayya RMAFC Cif Elias Mbam ya sanar da cewa,  hukumar dake tarawa gwamnatin tarayya haraji ta kasa FIRS ta samar da kashi 59.7 bisa dari ga asusun gwamnatin tarayya a cikin watanni uku da suka wuce.

A cewar Shugaban hukumar tara kudade ta tarayya RMAFC Cif Elias Mbam, hakan ya kuma nuna cewa, kudaden sun kai sama da rabin adadin abinda aka tarawa gwamnatin tarayya.

Cif Elias Mbam wanda ya sanar da hakan a lokacin da ya kai ziyarar aiki a shalkwatar hukumar FIRS dake a babban birin tarayyar Abuja tare da kwamimishinonin da kuma wasu mahukuntan  hukumar RMAFC ya ci gaba da cewa, hukumar ta  FIRS ita ce a kian gaba wajen tura kudi a cikin asusun na gwamnatin tarayya.

Ya kara da cewa, yawan kudin da hukumar ta tura a cikin asusun na gwamnatin tarayya a cikin wata uku da suka shie sun kai kimanin kashi 59.7  a cikin dari.

Ya yi nuni da cewa, rabin kudaden da ake turawa matakan gwamnati uku dake a kasar nan, suna fitowa ne daga hukumar ta FIRS  kuma a saboda wannan kokarin naku ina mai jinjina maku.

Shugaban hukumar tara kudade ta tarayya RMAFC Cif Elias Mbam  hukumar tasa ta RMAFC da kuma hukumar  FIRS zasuci gaba da yin hadaka a tsakanin su, inda ya kara da cewa, shugaban hukumar ta FIRS  a cikin watan Yuni kana wajen da aka rantsar da yayan hukumar ta RMAFC kuma tuni, duk sun  kama aiki.

A cewar Shugaban hukumar tara kudade ta tarayya RMAFC Cif Elias Mbam suna kuma bukatar su fahhinci  sauran manyan masu ruwa da tsaki da hukumar ta RMAF ke gunar da aiki dasu yadda zasu samu sauki wajen gudanar da ayyukan su, musamman ganin cewa, hukumar ta FIRS, ita ce babbar mai ruwa da tsaki ga hukumar ta RMAFC.

Shugaban hukumar tara kudade ta tarayya RMAFC Cif Elias Mbam ya ci gaba da cewa, “Munzo nan ne don mu fahimci ayyyukan da kuke gudanarwa, mu samman doin mu san fannin da zamuyi hadaka daku, inda hakan zai taimakawa gwamnatin tarayya samar da kudaden shiga.”

A cewar Shugaban hukumar tara kudade ta tarayya RMAFC Cif Elias Mbam, “ Muna kuma son sanin fannin da zamu taimakawa hukumar ta FIRS.”

Shi kuwa babban shugaban hukumar  FIRS  Tunde Fowler a nashi martanin ya ce,  hukumar sa  FIRS zata ci gaba da yin iya kokarin ta wajen tara kudin shiga don a dinga turawa matakan gwamnati uku dake a kasar nan.

A cewar babban shugaban hukumar  FIRS  Tunde Fowler Fowler “ Mun samar da hanyoyin fasahar zamani yadda zamu sauki wajen tara haraji, inda ko daga gida ko ofis za’a iya biyan harajin ga hukumar ba tare da sai anzo ofis dinta ba.”

Shugaban hukumar  FIRS  Tunde Fowler yaci gaba da cewa, “ Muna sane a akwai butar a kara yadda ake tarawa gwamnatin tarayya haraji kuma zamu ci gaba da yin iya kokarin mu wajen tura kudi ga matakan gwamnati uku dake kasar nan.”

Da yake mikawa Shugaban hukumar tara kudade ta tarayya RMAFC Cif Elias Mbam littafi a kan tara kudin shiga taken “ Mai biyan haraji shi ne sarki” Shugaban hukumar  FIRS  Tunde Fowler Fowler ya sanar da cewa, sunyi amfani da littafin wajen nuna irin kokarin da shugaban kasa Muhammdu Buhari yake yi a kan tara haraji.

Ya kara da cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna a zahiri yana da kishi da kuma kaunar  Nijeriya.

A cewar Shugaban hukumar FIRS  Tunde Fowler, irin salon shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari  muke yin amfani dashi a hukumar ta FIRS, kuma duk mun daukarwa kawunan  mu dole ne mu nuna son aikin mu, musamman don mu bayar da tamu gudunmawar wajen ciyar da kasar nan gaba.

Exit mobile version