Abubakar Abba" />

Kashi 70 Na ‘Yan Gidan Yari Ana Tsare Ne Dasu Ba Bisa Ka’ida Ba – PRAWA

Kimanin kashi 70 bisa dari na mutanen da ake tsare dasu a gidan kaso dake a daukacin fadin kasar nan ana tsaredasu ne ba’a bisa ka’idar da doka ta tanadar ba.

Wata jami’ar kungiyar  dakekula da walwalar wadanda ake tare dasu a gidan Yari PRAWA Barista  Katume Mohammed ce ta sanar da hakan a lokacin da take yin jawabi a wani taro da aka shiryawa yan jarida masu rahotannin yancin yan adam dake a jihar Kano da wata kungiya mai zaman kanta ta shirya a jihar.

Ta kuma koka a kan yadda ake ci gaba da samun cunkoso a gidan Yarin dake a fadin kasar nan, inda ta yi nuni da cewa, mafi yawancin wadanda ake tsaren dasuana tsrae dasu ne ba’a bisa doka ba kuma yawancin su laifukan da suka aikata basu kai matsyin a kaisu gidan Yarin ba.

A cewar ta, yawancin sun aikata laifukkan da ake tsare dasu ne saboda kangin talauci da ya dame su, inda kuma ta yi kira ga mahukunta dake kasar nan da kuma masu ruwa da tsaki dasu samarda mafitar data dace don magance hakan.

Barista  Katume Mohammed  ta ci gaba da cewa,“Ya zama wajibi gwamnati ta banbance a kan aikata manyan laifukka da kanana, musamman ganin cewar ana kulle mutane a gidan Yarin alhali basu aikata laifukkan da ya kai matsayin a kaisu gidan Yarin ba.”

A cewar Barista  Katume Mohammed, kulle sun da akeyi a gidan Yari hakan yana janyowa gwamnati tana kashe kudade masu yawa wajen ciyar dasu, domin babu ta yadda zaka kulle mutum san nan kaki ciyar dashi abinci.

Shima wani mai ruwa da tsaki a nasa jawabin a gurin taron Mista Christian Osueke ya yi kira ga alumma su rungumi dabi’ar chanza rayuwar su don zamowa mutane na gari.

Exit mobile version