Ministan Lafiya da Jin Dadin Jama’a, Farfesa Muhammad Pate, a ranar Laraba ya ce marasa lafiya sun gamsu da cibiyoyin kiwon lafiya da ayyukan kiwon lafiya a matakin farko, inda ya ɗaura mizanin gamsuwar a kashi 74 cikin 100.
Pate, wanda ya bayyana haka a taron shekara-shekara na shekarar 2025 na Bitar Ayyukan Lafiya ta Hadin gwiwa ta 2025. ya kara da cewa, amincewa da alkiblar tsarin kiwon lafiya ya karu zuwa kashi 55 cikin 100.
Wannan taron bitar, yana daya daga cikin muhimman tarukan ɓangaren kiwon lafiya a Nijeriya, inda take tattaro masu ruwa da tsaki don duba ci gaba, tantance aiki, da nazarin muhimman abubuwan da suka fi dacewa a mayar da hankali a shekarar da ke tafe.
A jawabinsa, ministan ya bayyana cewa, binciken jin ra’ayin ‘yan kasa a fannin kiwon lafiya da aka gudanar a shekarar 2023, 2024, da 2025 ya nuna sakamako mai karfafa gwiwa.














