Mustapha Ibrahim" />

Kashi 80 Cikin 100 Na Bukatar Ruwan Sha Gwamnatin Yobe Ta Samar Da Shi -Injiniya Wakili

Daga Mustapha Ibrahim, Kano

An bayyana cewa yanzu haka kasha 80% cikin 100 na bukatar tsaftaccen Ruwan sha ga al`ummar Jihar Yobe, Gwamnatin Jihar Yobe karkashin jagoracin Ibrahim Gaidam ta samar da shi domin amfanin Al`Ummar Jihar Ta Yobe.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Injiniya Muhammad Surajo Wakili kwamishinan albarkatun Ruwa na jihar Yobe a yayin da yake yiwa manema labarai Jawabi bayan kamala wata bita da gwamnatin Yoben ta shirya akan bunkasa Hanyoyi samar da wadataccen Ruwan sha da makamantansu da aka gabatar a birnin Kano, a wannan lokaci da ya gabata.

Haka kuma ya kara da cewa duk da ya ke aikin ruwan da ake samarwa a Jihar Yobe yawanci ba daga koguna ko dam-dam ba ne, kamar yadda ya ke a nan Kano da wasu jahohi da za`a ce ga yawan litar da ake samarwa a kowacce rana ko Lissafin Wata Ko Shekara, Tunda Yawanci A Jihar Yobe Gwamnati tafi samar da Ruwan sha ta hanyar haka Rijiyoyin zamani masu samar da ruwa domin amfanin al`ummar jihar su ta yobe to amma dai yanzu haka an samar da Ruwa don amfanin mutane kasha 80 zuwa 90 da mutanen Jihar ke bukata.

Danga ne da matsalar tsaro kuwa da Jihar take fuskanta kuwa ya ce idan an samu wani gari da ya ke da matsala ta Ruwa ko hanya ko makarantu da makamantansu to da zarar an samu tsaro a garin to duk wata ma`aikata da take da aiki a garin to taron dangi suke a garin ma`aikatar Ruwa na aikin samar da Ruwa, haka ta ilimi na gina makaranta ta ayyuka na aikin hanya wannan shi ne abinda su ke yi don warware matsaloli al`ummar su ta Jihar Yobe a cewar Injiniya Muhammad Surajo wakili kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar.

Exit mobile version