Muhammad Awwal Umar" />

Kashi 97 Na Cututtukan Yara Na Da Alaka Da Cizon Sauro – SFH

An bayyana cewar kusan kashi tis’in da biyar na cututtukan da ke yaduwa a kasar nan su na da alaka da cutar cizon sauro. Wanda dole sai an yaki zazzabin cizon sauro kafin a iya kauda kananan cututtukan da ke addabar jama’a.

Jami’in da ke kula da harkar sadarwa ta kungiyar tsarin kula da lafiyar Iyali ( SFH), Mista Daniel Denel Gboye ne ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai na shirin yaki da cutar cizon sauro da rarraba gidan sauro ga al’umma. Wanda shiri ne na yaki da cutar cizon sauro na kasa da hadin guiwar kungiyar kula tsarin kiwon lafiyar Iyali, NMEP/SFH, wanda aka shirya a dakin taro na hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko.

Shirin rabon gidan sauron wanda zai shafi jahohi uku da suka hada da jihar Kaduna, Kano da Jihar Neja, yunkuri ne na magance irin rahotannin da ake samu kan cizon sauro da yaduwar wasu cututtukan akan matsalar cizon sauro.

A shekarar 2009, gwamnatin tarayya ta rabar da gidan sauro 57, 773, 191 a jahohi talatin da shida har da Abuja.

Shirin rarraba gidan sauron da zai gudana cikin kwanaki biyar a dukkanin kananan hukumomin jihar Neja, za a fara shi ne bayan an gama tantance wadanda ya kamata su anfani da gidan sauron daga yankin kananan hukumomi da yankunan karkara.

Shirin rabon gidan sauron wanda zai kunshi karban bayanan mutum ta hanyar tsarin Data Collection wato tattara bayanai ta hanyar na’ura mai kwakwalwa, zai taimaka wajen ganin kowani mutum biyu sun anfana da gidan sauro wanda komai yawan gida ba za su kasa samun gidan sauro guda hudu ba.

Hukumar dai tace a wannan shekarar shirin rabon gidan sauron ya ta’allaka ne kawai akan magidanta.

Darakta mai kula da wayar da kai akan kiwon lafiya a jihar Neja, Dakta Ibrahim Idris, ya jawo hankalin jama’a kan baiwa shirin hadin kai dan kau cutar zazzabin cizon sauro a jihar, yace yanzu haka kusan duk kananan cututtukan da kebl addabar yara ‘yan kasa da shekaru biyar, kashi tis’in da bakwai yana da nasaba da cutar cizon sauro.

Yace hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya ( WHO) ta bada tabbacin kowani gidan sauro zai iya aiki na tsawon shekaru uku. Dan haka akwai bukatar yin anfani da gidan sauro tsawon awanni ashirin da hudu.

Hukumar kiwon lafiya ta kasa ta bayyana cewar ta dauki shirin yaki da cutar cizon sauro a kasar saboda irin barazanar da yakewa lafiyar al’umma, wanda kusan cutar a kowani shekara tana zama barazana musamman ga kananan yara da mata masu ciki wanda barazar cutar ta zamo wata hanya ta salwantar rayukan jama’a, dan haka muna da burin ganin cutar cizon sauro ta zama tarihi a kasar nan.

Exit mobile version