Kashi Na Biyu: “Yadda Mutum Zai Kare Kansa Daga Fadawa Tarkon ‘Yan Siddabaru”

Bambancin Siddabaru Dabo Da Surkulle

Yan Siddabaru

Wannan ita ce tattaunawar da wakilinmu SABO AHMED KAFIN-MAIYAKI ya yi da masani MALAM UMAR GUGA a kan Siddabaru kashi na biyu. Kamar yadda muka yi muku alkawari a makon da ya gabata, ga karashenta wadda take dauke da bayanai masu muhimmanci kamar yadda RABI’U ALI INDABAWA ya rubuta.

 

 

To akwai wani karin haske da za ka yi wa mutane dangane da yadda za su fahimci shi wannan Siddabarun, da zai zama sun guji tarkon fadawa tarkon masu Siddabarun?

To na farko dai mutum ya samu ilimi, kuma ilimi mai inganci. Kamar ni dai Musulmi ne, ilimin Addinin Musulunci shi ne dai ginshikin rayuwa. Idan ka same shi zai kokarin taimaka maka na harkokin rayuwa, duk abin da za ka ga an yi ka dogara ga Allah cewa wannan abu ya ake mallakar sa, kai ka san in za ka mallaki abu ta hanyar saye ne ko gado, amma duk wani abu da za ka bi ta hanyar hikima ka yi kaza-kaza haramun ne ba’a son sa, sai dai ka yi kokari in kasuwanci za ka yi, ka yi in kuma noma za ka yi ka yi, in kuma saye za ka yi ka sayar ko fatauci ka yi, amma yanzu kana zaune kawai wani ya zo shi ba banki ba ya zo ya ce zai fada maka hanyar da ake kudi, ka ga wannan haramtacciyar hanya ce.

Wadansu kuma rashin ilimi ke jan su ko mene ne za su iya yi in dai za su samu abin duniya, to a samu ilimin addini in kai Musulmi ne ka yi amfani da koyarwar da ka samu ta Musulunci, in kuma kai Kirista ne ka yi amfani da koyarka ta Kiristanci. Don ka san ko Bamaguje a kasar Hausa ba ya sata bai yarda da sata ba, to ka ga ko addinin gargajiya da ake ganin ba na Allah ba ne bai yarda da irin wadannan abubuwa da ake yi ba. Maguzawa da suke dauko amfanin wannan su dawo da shi wurinsu sun san ba daidai ba ne.

 

Shin akwai banbanci tsakanin Siddabaru da Dabo?

Duk abu daya ne, ai Dabo a ce an yi maka wani abu, yanzu akwai wanda zai maka Dabo ya yi maka mota. Akwai wani mutum a can yankinmu a Bakori, zai yi maka mota lafiya lau, kirar Jeep da sauransu, za a yi ciniki ka ba da kudi da komai, amma daga karshe za ka ga ta koma an daddaura kara. Ko kuma yanzu a yi maka Dabo ka ba da kudi kalilan a yi maka shanun miliyoyin Naira a ce ka kora su, ka ga san banza ce ta kawo ka, to sai a kawo maka wasu ka’idoji da ba za ka iya cika su a gindaya maka, sai a ce to yanzu wannan shanun ka tafi da su kada ka yarda su gudu kada kuma ka takura su, kar ka yarda su tarwatse. To da ka fara tafiya suka yi harr din nan kana binsu sai ka ga sun koma tsummokarai. Ka ga Dabo ma yana da tushe a kasar Hausa sosai da sosai saboda shi suka fara yi, ka ga ai Siddabaru akwai abu na ilimin addini da suke sakawa, to amma shi Dabo. Akwai wani kauye kusa da mu nan ‘Yar Mai Dabo, su Mai Dabo ma ake ce musu mun yi iyaka da su, to da Siddabarun da Dabo dukkansu suna tafiya ne da juna.

 

Wata kalma da take yawo a bakin mutane Surkulle, shin me wannan kalma take nufi?

Surkulle wani abu ne da za ka ji an hada shi ba kai ba gindi, ai za ka ji yawancin ‘Yan bori su suke wadansu maganganu sai ka ji an ce kai wannan Surkulle ne, sai ka ji mutum ya kira ka da sunan da ba naka ba, wanda aka yi wa Girka kenan, ko kuma a dauko wani da wani abin a hautsina shi ka ji wata maganar da ake yi sabanbotai, wato ma’ana ka ji ana magana ba kai ba gindi sai ka ji an ce wannan surkullensa ya yi yawa. To kuma shi kansa surkullen ai wani nau’i ne na tsari shi ma, tun da za a zo a yi maka ne a sirka da kaza da kaza, ajinsa iri daya da wancan, hakan na suke amfani da wannan hikimar domin su cimma burinsu amma ta gurbatacciyar hanya. Ko kuma ni a tasirin Musulunci ne ya sa na ce haka amma su masu yi ba sa ganinsa a matsayin gubatacciyar hanya, suna yin sa ne a yadda suke ganin suna tafiyar da rayuwarsu.

 

Yanzu dai idan na fahimce ka da Surkulle da Dabo da Tsafi duk daya ne kenan?

A’a ai tsafi kat ne, duk a samansu yake, ai ka ji Bahaushe ya ce in ana dara fidda uwa ake. A duk wadannan abubuwan da ka ga ana yi matsafa ne ke yinsu dukkansu karkashin tsafi suke, yanzu kai Musulmu ne amma ba za ka iya yi ba ko. Ka ga ko da kana yi za ka daddama, domin ka san Musulunci ya haramta. Idan muka je bincike a kan Maguzawa duk da dai kalmar Maguzawan tana dan rudani a ce wa mutum Bamaguje.

 

Rudani kamar yaya?

Yawwa rudani kamar wadansu, ka san ita kalmar Bamaguje tana nufin wanda ya ki Sallar gaba daya, ba ya Musulunci su ne Maguzawa, amma kuma sai ka ji mutane na cewa wai mutum ya bar Maguzanci ya koma Kirista, ko kuma ya koma Musulunci sai ka ji ana Bamaguje. To su kansu wadanda suke alfahari da gadon nasu, in muka je muna tambayarsu muna boye cewa, kun ga wannan al’adu ba a so ake yi, sai su ce kai ina yi, me kake so na yi ma yanzu, gadona ne babu abin da na gada bayansa. A cikin Katsina akwai wurare tsibi-tsibi da suke alfahari da wannan gadon nasu.

To shi tsafi shi ne dai kan gaba a kasar Hausa, to matsafa su ne suke aiwatar da irin wadannan abubuwa amma kuma akwai masu Sallah akwai masu zuwa Coci wadanda suka gina rayuwarsu kan wannan, an shiga rigar addini ana yin su ko don neman dan abin duniya.

 

Wannan bincike naka ina da ina ya kai wanda kai mamakin shiga wuraren?

To wannan bincike dai, gaskiyar lamari ya kai ni wuraren da a yanzu haka in kana da Naira biliyan daya ko Tiriliyan uku ba za ka iya zuwa wurin ba, domin wurare ne da dama ‘yan ta’addar nan sun mamaye, kuma duk wannan bincike da nake yi ma a yanzu haka ina shiga wuraren da ake cewa ana yin irin al’adun nan da ake cewa na da, to ba fa na da ba ne har yanzu na yanzun ne, don sau tari za ka je wurin Danbori ka ga mutane a wurinsa yadda ka san likita haka yake, wane ya kwana kansa na ciwo a bashi magani kaza wani a bashi sa’a, abu ne har yanzu yana cin kasuwarsa sosai-sosai, sai dai an shiga wata da aka saka ta.

Kuma hana rantsuwa, akwai tasirin Musulunci, wanda za ka ji an ce ai iskar ma malami ne, ko ai iskar ma Alhaji ne, ai iskar ma Musulmi ne ko kuma Kafiri ne, wannan fari ne, wannan baki ne, to muna ganin abubuwan ban mamaki in mun shiga, kuma har yanzu mutane suna aiwatar da wadannan abubuwa wasu aksari.

 

To a karshe wane sako kake da shi na jan hankali musamman ga al’umma ganin ba su fada wannan tarko ba?

Kiran dai shi ne imani da Allah, shi ne mai bayarwa shi ne mai hanawa, kuma ka sani, mu’amalarmu ce da hanyar cimmu da hanyar kasuwancimmu ne suka gurbata. Kudi ne na ruwa yanzu ba a tantance su, abin da za a ci ba a gane ya aka same su kawai nema ake a ci. To dama shi neman tara abin duniya shi ke jefa mutane halaka iri-iri, wasu kuma mulki ne kawai a gabansu sun riga sun samu abin duniya, ta yaya za a samu mulki, in ka je wurin matsafi zai ce ka samo min kan abu kaza da kaza da sauransu sai an batar da kai, kuma duk wannan abin da za ka samo wallahi in Allah ya ce ba za ka yi ba, ba ka isa ka yi ba. In kuma Allah ya ce ka yi ko ba ka yi za ka yi.

To mu ji tsoron Allah, domin wani fa ba kansa zai yi wa ba, wani zai yi wa don kada ya samu wani abu, kawai ya wahalar da kansa a rayuwa, to sai mun cire wa kanmu kwadayi da hassada sai ka ga mun zauna lafiya in mun yi addu’a sai Allah ya amsa.

 

Masha Allah muna godiya

Ni ma na gode

 

Exit mobile version