Kashi Na Farko: Yadda Ake Amfani Da Siddabaru Wajen Damfara Da Hanyoyin Bankado Masu Yi  

Siddabaru

Kowa ya san irin yadda ayyukan ‘yan siddabaru ke addabar al’umma saboda yadda suke amfani da hakan wajen damfara. Sau da yawa, ana samun mutanen da hankulansu ke gushewa ko samun tabin-hankali bayan ‘yan siddabaru sun damfare su. Saboda wannan matsala da ta addabi al’umma, LEADERSHIP HAUSA, ta leka Sashin Nazarin Harsuna Da Al’adun Afirka da ke Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, domin  gudanar da bincike kan yadda ake amfani da siddabaru wajen damfarar jama’a da kuma yadda al’umma za su kubuta daga fadawa tarkon ‘yan damfara masu yin siddabaru.

Wakilinmu SABO AHMAD KAFIN-MAIYAKI, shi ne ya shiga Jami’ar, inda shugaban Sashin Nazarin Harsuna Da Al’adun Afirka, DAKTA SHU’AIBU HASSAN, ya hada shi da wani babban dalibi mai karatun digiri na uku, MUHAMMAD UMAR GUGA, wanda ya yi karatun digirinsa na farko a Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato, kan Al’adun Hausa da tasirin noma a kan sunayensu, irin su, Ci-wake da Taroro da makamantansu. Daga nan ya dawo nan Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, inda ya yi digirisa na biyu a kan tsafi a kasar Katsina da kuma bautar iskoki, amma duk da cewa, an yi wannan binciken ne a kasar Katsina, amma an bibiyi na wasu sassan kasar nan, inda aka samun damar kammala wannan aiki a shekara ta 2019. Yanzu haka kuma, cikin ikon Allah yana didirisa na uku, inda yake bincike a kan tunanin Bahuashe game da iskokin tudu da na ruwa. Ga dai tattaunawar kashi na farko kamar haka:

 

 

 

Masu karatu za su so ka gabatar da kanka gare su…

 

Ni sunana Muhammad Umara Guga, mutumin kasar Bakori

 

To gashi mun hadu da kai a Jami’ar Ahmadu Bello a Sashen Narin Harsuna da Al’adun Afrika, meye makasudin zuwanka wannan wuri?

 

Ni dalibi ne a wannan sashe, na yi karatun Digirina na farko a Jami’ar Danfodiyo a bangaren al’adun Hausawa, da ya shafi sunayensu da tasirin noma, da a kan irin su Siwatataroro da dai makamantan wadannan sunaye na gargajiya. Sannan kuma na zo a wannan sashe na Zariya, wannan sashen harsuna da al’adun Afirka na yi Digirina na biyu a kan Tsafi a kasar Katsina, Tsafin kuma shi ne bautar iskoki, tsafin budurwa da uwar gona shi aka kalla. Amma wannan duk da an yi shi a kasar Katsina, to kuma an bibiyi na wasu kasashen Hausa wanda aka yi bitarsu aka samu aka yi wancan aiki aka gama shi a shekarar 2019, a yanzu kuma cikin ikon Allah an dora a kan abin da ake yi ana kokarin bincike a kan iskoki, tunanin Bahaushe a kan iskokin ruwa da na tudu, shi ne ake ta kokarin a fara aikin in sha Allahu.

 

Tun da ka yi maganar iska, akwai maganar siddabaru, me za ka ce da masu karatunmu a kan abin da ya shafi Siddabaru?

Na’am Siddabaru wata hanya ce wadda a iya cewa kowacce al’umma ta duniyar nan tana da hanyar da take aiwatar da abinta. Siddabaru abu ne da za a zo a yi maka wanda za ka ga ya shallake hankalin mai tunani, da wanda bai san abin ba. Za a zo nan take za ka ga mutum kuna tare da shi ya cire kansa ya ajiye shi, amma a gaskiyar lamari ba kan nasa ya cire ba, duk wanda ya cire kansa in har kan ya ciru to ya ciru kenan har lahira.

To dukkan kabilu na duniya suna da hanyoyi nasu na Siddabaru, mutum zai yi amfani da wata hikima ko dabara, wadda za a kawar ma mai tunani tunaninsa a shallake wannan tunani nasa a aiwatar da wani abu da ido bai gane shi, tunanin mai tunani bai iya tunani yadda ake yin sa , in har dai ba a kan wannan hanyar ka ginu ko kake yi ba ko ka samu illarsa. Wannan shi ne Siddabaru.

 

Shin Siddabaru yana da nau’i-nau’i daban-daban ne ko kuwa nau’i daya ne ake amfani wajen gudanar da shi?

A’a yana da nau’o’i daban-daban mana

 

To kamar yaya nau’o’in nasa suke?

Yanzu ko tuwo ba akwai na dawa, akwai na masara, akwai na gero ba, to Siddabarun shi ma ya danganta, iri-iri ne, akwai Siddabarun da za a yi maka, ko za a yi wa wanda ake son a yi wa na a damfare shi kudi, akwai Siddabarun da za a yi wa wani da ake so a haukatar da shi, akwai Siddabarun da za a a yi a razana mutum, akwai Siddabarun da za a yi da iskoki za a hada, akawi kuma Siddabarun da za a hada da itatuwa, sannan akwai Siddabarun da za a yi da wasu halittu wadanda suke zagaye da mu.

 

Yanzu ana iya daukar Jemage ko Kadangare a yi wani Siddabaru da shi wanda ake so a yi ma a cimma bukata da shi kuma ai masa. Su kansu masu Siddarun sun kasu kashi-kashi; akwai wanda ke amfani da Siddabaru don ya samu mabiya, akwai wanda yake amfani da Siddabaru don ya samu buwaya a ji tsoronsa cikin al’umma, akwa kuma wanda zai yi don ya taimaki wani. Yanzu za ka ga wani ya dauko ganye ya mittsika sai ka ga goro, sai ka je ka ci, sai ya yi haka sai ka ga kudi kuma ka je ka kashe, amma  zahiri fa ba ya amfani da wannan abin.

 

To me ya sa shi ba zai yi amfani da su ba tun da kudi ai ya kamata ya kashe su?

To ai ba na gasikya ba ne, a yadda tsarin Siddabaru ya taho da yadda aka hada shi in har za a rika Siddabarun na gaskiya ai ka ga da yanzu ba kanta, kowa sai ya je ya yi Siddabaru ya rika yin kudi yana kashewa, amma in da a ce shi zai rika amfani da su ai ka ga da magana ta lalace, sai dai in ya yi ya baka kai ka je ka yi amfani da su. To kuma ka ga da yake Allah Sarkin baiwa ne a ko da yaushe yakan kare bayinsa, wannan abin ga shi ana yin sa amma su kansu mutanen da ke aiwatarwa ma suna da wani tunani na musamman cewa ba gaskiya ba ne, ko da za a yi ma a razana ka don cimma wani buri.

A wani lokaci ba na mancewa Allah ya jikan mahaifinmu, yana da sarauta a kauyenmu, ana nan sai ga wani mutum ya zo wurinsa, sai ya rike hannunsa, da ya rike hannunsa, sai irin kamar wuta ta ja shi, ya yi wata irin kururuwa, sai ya ce ya bude hannun, yana bude hannun sai ya ga bakar laya da wasu allurai masu gashi, ya ce ai ranka ya dade an so a kashe ka, aiwannan abin da aka yi maka da ba za ka yi sati ba za ka bar duniya. To ka san halin mutane kowa da irin tunaninsa, ina nan aka yi min magana, ina tabbatar maka ina yaro fa a wannan lokacin ko Jami’a ban kai ga shiga ba, amma ina zuwa muka hada ido da mutumin nan ya sunkuyar da kai. Sai na ce masa ni ma ina da larura, ina jin wani abu na yi min yawo kaza-kaza, kuma na fada masa gaskiyar labari, mutumin nan dai ya shiriritar da wannan magana tawa gaba daya bai waiwaye ni ba. Na ce ranka ya dade ka ga wannan mutumin dan damfara ne, wannan Siddabaru ne ba gaskiya ba ce, yanayin ‘yar dabara ce don ya samu abin da zai samu, ka ba shi ya je ya yi amfani da shi, amma ni na so a ce ya gaya min maganin matsalar da take damuna, to shi haka Siddabaru yake.

Akwai kuma Siddabarun da za ka ga an je an kuma samu mutanen da suka yarda da shi a wurin an yi musu duk abin da ake so an bar wurin. To ka ga Siddabarun akwai na tsaro wanda mutum zai kare kansa da shi, zai ma wani Siddabarun in ka taho ka hango gidansa akwai mutum a tsaye, ko akwai mutane suna kallon ka, barawo zai dauka ana kallonsa kuma hikima ce kawai aka yi, galibi akwai wanda ake hadawa da itacen Tumfafiya, to ka ga akwai tsaro kenan. To akwai na neman abin kai, wanda za ka ga ni masu Siddabarun ne da kansu za su je kasuwa su yi kaza da kaza sai ka ga tattabara ta tashi da sauransu, duk neman kudi ne.

 

Kuma Siddabarun da za ka ga an cutar da mutum, yanzu za ka ga in an ga dama a sakar wa mutum Siddabarun cutar da za ka ga yanzu ta dame shi, har sai ya dawo wurin wanda ya yi masa wannan Siddabarun sannan a yi masa magani, dama wata hikima ce aka yi aka daure wani abu ko aka matse wani abu sai an dauke shi an lalata shi sannan ka ga mutum ya samu waraka kan wannan Siddabarun da aka cutar da shi.

 

Ka fado nau’o’i na Siddabaru, shin meye bambancin Siddabaru da Tsafi?

Yawwa shi tsafi abu ne wanda ake bautarsa, shi ai shakurukundum ne, za su ware kaza sai su bauta masa, iska kaza ko dabba kaza, shi kuma Siddabaru, wani nau’in abu ne da yake fitowa daga abin da ake tsafawa. Yanzu in wasu suna amfani suna bauta wa iska wuri kaza, suna iya amfani da wasu abubuwa na iskar nan domin su yi wani Siddabaru. Kamar yanzu manoma, misali in ka samu manoman da suke tsafi na noma, suna bauta wa wani ko wata iska ta daban misali, a ce ko Remi, ko Gajimari ne, ko Doguwa ce ko Barhaza, ko Duna, su ne galibi Arna wadanda suke tsafin noma suke amfani da su, to za su iya amfani da wani bangare na tsafin nasu su yi Siddabarun kare nomansu, ko kuma su yi Siddabarun kar a cutar da wannan gonar, ko kuma amfani da shi ta yadda amfanin makotansu ba zai yi kyan nasu ba, to suna irin wannan tsarin, to amma shi mai Siddabaru yana amfani da tsafi ne don ya cimma burinsa wajen aiwatar da Siddabarunsa. Ka ji abin da ke faruwa .

 

Akwai wata dangantaka tsakanin Siddabaru da tsafi?

Akwai mana, to yawancin matsafa ai su suke yin sa, ai yanzu misali idan ka gano mai Siddabaru, farko abin zai yi za a ce ai wancan mushiriki ne, wancan ai matsafi ne, to ka ga wannan tsafi shi ne tsanin da za ka fara hawa domin ka samu gindin zaman da za su kai ka abubuwan da za ka yi tsafi  koko abubuwan da za su kai ka ka je ka yi Siddabarun, tun da ma su Siddabaru ai sun yi imani da shi wanda bai imani da shi ba ba zai yi ba. To ka ji alakarsu.

 

Da ka yi magana a kan yadda ake siddabaru a harkar noman, baya ga harkar noman akwai wata harkar kasuwanci ko wani abu na gargajiya da ake amfani da siddabarun wurin yin sa?

Kwarai kuwa, ai yanzu kamar kasuwanci akwai Siddabaru sosai, akwai Siddabaru na kiran kasuwa. Akwai Siddabarun da za a iya yi wa mutum zai zo abokin sana’arsa ne ku kasa kaya da shi, shi na sa za a ga kamar ya rube kuma ba rubabbe ba ne mai kyau ne, amma sai an gama sayen naka, in ya ga dama sai daga baya a duba a ga a’a ashe wannan ma ba rubabbe ba ne, in ko bai ga dama ba ba mai sayen naka.

 

Amma ta yaya za ka gane cewa Siddabaru aka yi maka?

To masu ilimin abin, ai ka ga da farko mun yi magana cewa abu ne da yake shallake hankali da tunani, kuma mai tunanin nan da hankalin duk yadda za kai masa bayani cewa karya ne ba zai yarda ba. To amma idan aka samu mai ilimin abin ya zo ya karya abin ka gani to za ka iya yarda. Kuma sannan matakin farko dai ilimi, ka ga wanda ya ilmantu da ilimin addini ko kuma na boko wanda zai iya bashi tunani mai kyau da zai iya gane kaza da kaza, ka yi wasu tambayoyi a kan siddabarun ma ka gani, in an ce Siddabarun nan gaskiya ne to mutum ya gina banki a gidansa mana ya ajiye ya rika kashe kudi, ka ga ba za ta yiwu ba, to irin wadannan abubuwa su ne za ka ga masu karyata shi suna ta yin tambayoyi, amma shi inda ake gane Sidadabaru za ka ga dai hikima ce ko an yi abin ba ya tabbata a rayuwa.

 

Za mu ci gaba mako mai zuwa idan Allah ya kaimu.

Exit mobile version