Connect with us

ADON GARI

Kashin Bayan Al’umma: Mata A Karamar Hukumar Kurfi

Published

on

Assalamu Alaikum, sunana Fadila H Aliyu Kurfi ‘yar asalin karamar hukumar Kurfi gaba da baya, Marubuciya kuma ‘Yar Jalida mai zaman kanta.

Duk da kasancewa ta marubuciya ban taba daukar alkalamina na yi rubutu kan siyasa ba amma wannan karon jiki na rawa zuciya na azama suka tilasta mani dole na yi tsayuwar aska domin kwato ma Mata ‘yancinsu, na dauki haramar shiga lunguna- lunguna da sako-sako domin taimakon mata’ yan uwana, wanda ba su da da muryar da za ta yi amo domin fada ma duniya halin da suke ciki, suna da koke suna da damuwa suna cikin wahala da kuncin rayuwa amma babu wanda za su kai ma koken a saurare su, za mu jawo su jiki mu tallata su duniya ta ji halin da su ke ciki, za mu zama tsintsiya domin mu share azzaluman ‘yan siyasa masu ci da guminmu wanda mu ke kasawa mu tsare mu raka a kirga lokacin zabe don kishinsu da kaunarsu kyauta domin akida kawai da kuma masu kudi da kansu kadai suka sa ni sai idan bukayarmu ta taso a nememu, ba mu da jam’ iyya ko daya sai wanda zai tallafe mu da yaranmu.

Babban dalila na fara tsoma baki a lamarin mata shi ne; zuwana Karamar hukumata Kurfi, tsananin kishin mata ya kara kaimi a zuciyata har na ji zan iya yin komai don ganin an tallafi iyayenmu da ‘yan uwansu bayin Allah mata, su ‘yan siyasar sai dai su taka kawunanmu su ci da zufar su sayi gida da motoci a shige birnin tarayya Abuja, sai lokacin zabe su kwaso jiki su dawo su watsa ma mutane ‘yar tsaba a kuma zabarsu, ‘yar tsabar ma sai wanda su ke da alaka da su ko da kuma wanda suke da alaka da mai rarrabawar, na sa ni tsaf suna mulkin kama karya tuni amma hankali na bai tashi ba sai wannan karon, dasu fa muke haduwa gurin zagin wasu azzaluman shugabanni amma kuma da sun hau sai su koma irinsu su manta da kowa da komai, sai hawan jirgirage a lula cikin duniya ayi kara’in wanda ba ayi ba zamanin kuruciya, haba shuwagabanninmu kudin da ku ke saka katin waya kadai ku kira wanda kuke so da zaku ware shi ku ba mata tallafin sana’a da ya ishesu har karshen rayuwarsu samun abin da za su ciki ma bakin salatinsu, ba fa irin zuka-zukan motocinku suke bukata ba a’a dan abin ci da sutura dan jari kawai, babu wannan sai dai ku yi lamo matsala da yunwa ta matsa ma talaka ya daga dan fili ko gidansu na gado ku saya a wulakance.

Na je karamar hukumata KURFI ziyara, kalar ruwan da suke sha kuma suke amfani dasu ruwan tafki ne idan rani ya zo rijiyoyi kafewa take yi, ga su da kauri kamar damammiyar fura, shekara da shekaru an kasa magance matsalar ruwa, tambayar da na fara yi ma kai na itace, ;wai duk Ciyamomi, ‘Yan majalisu har da na Dattawa wai! da suke mulki tun ina cikin zanen goyo idan sun kasa magance matsalar ruwa kadai me suke iya magancewa, me ye amfaninsu, haba Yaya Kantoma, Malam Dan Majalisar Jaha, Alhaji Dan Majalisar Tarayya da Baba Dan Majalisar Dattawa ko kun manta ne? Ruwan tafkin nan da kuka sha kafin mu ingizaku kan kujerunku ku fara shan ruwan roba har yanzu mutanenku na nan na sha, makarantun nan masu karyayyun kujeru wasu daliban ma a kasa suke zama, makarantun nan na babu gyara kuma su kuka yi fa, ko kun manta mu ku ka taka izuwa wannan mukaman, don kun san cewa kun makale kudadenmu ko safka kuka yi akan kujerunku ba za ku dawo mana ba bare a sha ruwan tafkin nan daku, kun ci ganye, kun mance sanda ake zama majilisa ana koken wasu da ku kuma gashi ana yin naku, mu fa ba gashe mura ba mu ke so ayi ba a’a a taimaka talaka ya kori talauci, ku tuna ba sayenmu ko ka yi ba ko dauki dora zabarku muka yi don ra’ayi, hannun da ya dangwala maku ranar zabe shirye yake ya dangwala ma waninku fa.

Dan Malisar Tarayya mun ji kana watsa ‘yar tsaba wacce ko darajar kudin da yaranka suke shan Askirin ba su kai ba, bayan kuwa mun san karfin samunka, nan ga ba da hotunan za mu hada rubutun, saboda abokanku na birni su ga yanda garuruwanku suke cikin halin ha’ ula’ i, kai kuma Baba Dattijo zaku zo neman kuri’unmu sannan zaku gane kan ungulu ya waye, da dan maganin da kuke tarfawa mararsa lafiya ai gara a basu jari yafi tunda dama ciwon kun san silarsa yunwa ce da wahala, Kantoma muna saka ido mu ga da me ka zo ku kai kuma, har yanzu dai shiru.

Shin idan idanunmu suka bude mu ka yi fito na fito daku, ta ya ya za ku kama ma shi kansa Mai girma Gwamna da Shugaban Kasa wurin kawo kujerun mata, Baba wadan nan wanda suke maka farfaganda su ne Kurfi, idan sun samu aljihunsu suke zubawa su yi Abuja idan suka ga dan garinsu na neman taimako su kira shi da dan mallaka, ba su da kima ko kwarjini a wurin ‘yan uwansu bare kuma’ yan gari, zasu fuskanci babban kalu bale ranar a fito, saboda Kurfi siyasar kishi muke yi ba ta sabo ko neman kudi ba, tsaf miji da mata da yaransu kowa zai zabi ra’ayinsa, ya ya zaku yi idan mata suka ki fitowa su zabe ku ko mu sabi alluna domin zanga-zanga dan duniya ta fuskanci halin matsi da mu ke ciki, duk wacce mijinta ya rasu gidanta ya rushe yaranta sun shiga garari, mata babu sana’a, ga zafin talauci da wahala da yara, idan an sako mace maza ku korata gida da yaranta ga talauci ga yunwa ga babu sana’a, ba mu da jam’iyya ba mu da gwani sai wanda ya rungume mu ya tallafemu, kar ku manta kunce, “mun fi maza yawa” wannan yawan zai mana amfani wurin kayar da ku ko taimakonku, ku tsumaye rubuta na duk sati a Jarida dauke da hotuna. Gyara mu ke nema da ‘yancinmu ba rigima ba. Kar ku manta; Mata Mu Ne Kashin Bayan Al’umma.

 

Fadila Kurfi ta rubuto ne daga Katsina, za a iya samun ta a fadilapeady@gmail.com

 

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: