Ranar Lahadi 3 ga watan nan na Satumba ne Allah ya yi wa fitaccen dan wasan kwakwayon nan da ke Kaduna, Alhaji Kasimu Yero rasuwa bayan ya yi fama da rashin lafiya, wanda kuma ya rasu yana da kimanin shekara 70, ya bar ’ya’ya takwas da jikoki goma.
Duk wani mai shekarun da suka kai 30 zuwa sama ba zai taba mantawa da Kasimu Yero ba, musamman wajen irin wasannin kwaikwayon da yake gabatarwa a gidajen talbijin na kasar nan, musamman gidan talbijin na NTA Kaduna, inda ya yi tashe a wasan nan nasa na KARAMBANA, wani wasa mai matukar ilimantarwa.
Haka kuma Alhaji Kasimu Yero ya yi fice a shekarun 1980 lokacin da yake fitowa a shirye -shiryen na NTA a wasannin ‘Magana Jari Ce’ (na Hausa da na Turanci), baya ga shirin da muka ambata na Karambana da dai sauransu.
Kasimu Yero ya rinka fitowa a matsayin Uncle Gaga a shekarun 1980 a shirin nan na Turanci, ‘Cock Crow At Down’ da kuma wanda ya yi na littafin Abubakar Imam, ‘Magana Jari Ce,’ wanda aka watsa a gidan talbijin na kasa, NTA.
Wannan rasuwa ta Kasimu yero ta girgiza al’umma, musamman masu harkar wasannin kwaikwayo, ballantana idan aka yi la’akari da irin rawar da ya taka a shirin nan na ‘Magana Jari Ce,’ shirin da ya yi tashe, ba a nan Arewacin kasar nan ba, ko sassan Kudanci, har a nahiyar Afrika. Sannan Kasimu Yero ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta al’adun Hausa a kasar nan.
Saboda yadda wasan kwaikwayo ya ratsa Kasimu Yero, ya kasance ko ba a fagen wasa ba, shi mutum ne mai ban dariya. Ya ma taba fadin cewa shi babban burinsa a kullum, shi ne ya sa jama’a farin ciki da dariya. Ta nan ne ma ya kasance shi mutum ne mai ganin ya cimma duk wani abu da ya sa a gaba.
Duk wadannan halaye na Kasimu Yero, ba halaye ne da za su sa mutum ya tara abin duniya ba, domin Kasimu bai rasu ya bar wata dukiya ba, amma ya bar mutuncin da kudi ba za su iya sayo masa shi ba. Ya gudanar da rayuwarsa cikin sauki, ya zauna lafiya da kowa, ya cika burinsa wajen sanya jama’a farin ciki da dariya duk inda ya samu kansa
Da wadannan abubuwa ne muke ganin cewa za a dade ana tuna Kasimu Yero, kuma za a dade ba a samu makwafinsa ba, musamman idan aka yi la’akari da irin yadda ya gudanar da nasa tsarin nishadantarwar, da kuma irin yadda masu nishadantarwa na zamnin yau suke gudanar da nasu. Shi ne ya Bahaushe ke cewa ‘Ba Rabo Da Gwani ba, Kafina A Samu Irinsa.’
Muna addu’ar Allah gafarta masa, Allah kyauta makwancinsa. Su kuma iyalan da ya bari, Allah ya yi masu albarka, ya kara masu hakurin jure wannan rashi.