Kasuwanci Na Raguwa Ne A Nijeriya Sakamakon Matsalar Tsaro – CBN

Bankuna

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bayyana cewa, karuwar rashin tsaro na shafar amincewar ‘yan kasuwa a Nijeriya da ma harkokin tattalin arzikin baki daya.

 

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan a yayin taron Kwamitin Manufofin Kudi (MPC) na ranar Talata a Abuja, inda ya bukaci karin kayan tsaro a muhimman wuraren samar da kayayyaki.

 

Gwamnan Babban Bankin ya kara da cewa, mummunan abubuwa ne tasirin rashin tsaro ke haifarwa a kan ayyukan da dole ne su habaka tattalin arziki da habaka karfin gwiwar kasuwanci.

 

Ya bayyana cewa, “Rashin tsaro ya yi tasiri ga kwarin gwiwar kasuwanci da duk harkokin tattalin arziki.

 

MPC ta bayyana cewa, da ayyukan rashin tsaro a muhimman wuraren da ake samar da kayayyaki, kuma ta bukaci Gwamnatin tarayya da ta kara sa ido kan harkokin tsaro a yankunan manoma.”

 

Gwamnan Babban Bankin ya bayyana cewa, mambobin MPC sun ba da kwarin gwiwa game da tasirin girbin abinci mai zuwa kamar yadda yake taimakawa ga hauhawar farashin kaya.

 

Ya kara da cewa, CBN zai ci gaba da sakin masara daga tanadin masararsa zuwa masu shuka a matsayin wani bangare na dabarun magance matsalar hauhawar farashin abinci da kuma daidaita farashin masara a fadin kasar.

 

Emefiele da mambobin MPC sun bayyana cewa, rashin ingantattun kayan more rayuwa na shafar hauhawar farashin cikin gida, don haka, suna sake nanata kiransu ga Gwamnatin tarayya da ta fifita saka jari a ayyukan jama’a.

 

“Za a iya samun kudin gudanar da irin wadannan ayyukan ta hanyar PPP da hadin gwiwar kasashen waje,” in ji shi.

Exit mobile version